Gwamnatin Tarayya ta sanar da ranakun hutun bikin Ƙaramar Sallah

Daga BASHIR ISAH

Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranakun Talata da Laraba masu zuwa a matsayin ranakun hutun bikin Ƙaramar Sallah.

Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo, shi ne ya ba da sanarwar hakan a rabar Lahadi.

Ministan ya yi amfani da wannan dama wajen taya al’ummar Muslmi na faɗin Nijeriya bisa kammala azumin watan Ramadan na bana, tare da fatan za a yi bikin Ƙaramar Sallah cikin lumana.