Zargin Dakatarwa: Magaji ya ɗaukaka kara kan hukuncin CCT

Daga BASHIR ISAH

Shugaban Hukumar Sauraren Ƙorafe-ƙorafe da Yaƙi da Rashawa na Jihar Kano (PCACC), Muhuyi Magaji, ya ɗaukaka ƙara bayan da Kotun Ɗa’ar Ma’aikata (CCT) ta dakatar da shi.

Kwamitin alƙalai uku ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Danladi Umar a Abuja, shi ne ya ba da umarnin dakatar da Magaji biyo bayan zargin rashin ɗa’a daga Hukumar Ɗa’ar Ma’aikata (CCB).

Sa’ilin da yake yanke karanto hukuncin, Alƙali Umar ya yi watsi da ƙarar Magaji inda ya ce kotun na da hurimin sauraren shari’ar.

Haka nan, ya unarci Gwamnan Kano, Abba Yusuf da Sakataren Gwamnatin Jihar (SSG) da su naɗa jami’in da ya fi cancanta don yi wa hukumar riƙon ƙwarya shugabancinta.

Bugu da ƙari, Alƙalin ya ce ba zai yiwu ba Magaji ya ci gaba da aiki a ofis a yayin da yake fuskantar shari’a don kauce wa yi wa shari’a katsalandan.

Sai a bisa rashin gamsuwa da hukuncin kotun, hakan ya sanya Magaji ta hannun lauyansa, Mr Adeola Adedipe, SAN, ya garzaya Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke Abuja.

A cikin ƙarar mai ɗauke da kwanan wata 5 ga Afrilu, Lauya Adedipe ya bayyana dalilai biyar kan dalilin ɗaukaka ƙarar da kuma buƙatar yin watsi da hukuncin kotun CCT.

Idan ba a manta ba, a ranar 16 ga Nuwamban 2023 hukumar CCB ta maka Magaji a kotun CCT kan zargin laifuka 10 da suka haɗa amfani da bayanan ƙarya da sauransu, lamarin da Magaji ya ce ba gaskiya ba ne.

Daga bisani an ba da belin Magaji kan Naira miliyan 5 da shaidu guda biyu.