Daga BASHIR ISAH
Gwamnatin Jihar Neja ƙarƙashin jagorancin Umaru Mohammed Bago, ta bai wa jami’an tsaro umarnin halbin duk wani tsageran da ya fito da makami da sunan daba ko hana al’umma sukuni a sassan jihar.
Shugaban Ƙaramar Hukumar Chanchaga, Hon. Aminu Ladan, shi ne ya faɗi haka bayan taron masu ruwa da tsaki na ƙaramar hukumar wanda aka yi a fadar Mai Martaba Sarkin Minna, Dokta Umar Faruk Bahago a yammacin ranar Asabar.
Shafin Tsalle Ɗaya mai bibiyar harkokin gwamnatin jihar ya rawaito Aminu Ladan ya ce, Gwamnan ya bada damar jami’an tsaro su yi amfani da bindiga a kan duk wani wanda aka gani da makami yana yi wa zaman lafiyar al’umma barazana.
Shugaban ya ce duk wanda ke tantama a kan wannan sabuwar dokar, ya gwada yi mata karan tsaye sannan ya ga sakamakon da zai biyo baya.
A cewarsa, ba za su taba lamuntar babban birnin jihar Neja ya durƙushe ba sakamakon aika-aikar ‘yan daba.
