Farashi zai ci gaba da tashi muddin gwamnatoci suka dinga biris da ‘yan kasuwa – Sardaunan Gwaram

Daga MOHAMMED ALI a Gombe

Saboda yadda farashin kayyakin abinci da na masarufi har ma da kusan komai a faɗin ƙasar yake ta ƙara wahal da ‘yan Nijeriya, baban ɗan kasuwan nan na Jihar Gombe, Alhaji Ahmed Abdullahi (Sardaunan Gwaram), ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da na jihohi baki ɗaya, da su tashi tsaye yanzun nan su ga sun bunƙasa kasuwanci a ƙasa.

Har illa yau, Sardaunan Gwaram ɗin wanda shi ne Mataimakin Sakataren Ƙungiyar Haɗin Kan “Yan Kasuwan Jihar Gombe, ya ce muhimman mafitar dai kenan wato gaggauta bunƙasa kasuwanci sannan tallafi ga “yan kasuwa musamman kamar waɗanda ya kira “tsaka-tsakiya da kuma na ƙasa”.

Alhaji Ahmed ya yi gargaɗi da cewa, muddin Gwamnatin Tarayya da na jihohi suka faskara suka yi burus da ingancin ‘yan kasuwa, to babu shakka farashi ya rinƙa hauhawa kenan kuma gaba kaɗan, talaka ba zai iya ciyar da kan shi ba ko da sau ɗaya ne a rana kuwa.

“Saboda haka, dole gwamnatotin jihohi da na Tarayya su yi duk iya yi su tallafawa ‘yan kasuwa su kuma gyaggyara masana’antu da kamfanonin sarrafa abinci da makamashi da duk abin da ‘yan ƙasa za su amfana da su sannan bugu da ƙari, a inganta tsaro a ƙasar baki ɗaya ta yadda kasuwanci zai gudana a cikin kwanciyar hankali,” inji shi a lokacin da yake tsokaci akan farashi da wakilinmu a babbar kasuwar Gombe a makon jiya.

Sardaunan Gwaram ɗin yana da tabbacin cewa, har idan aka bi waɗannan tsare-tsaren to babu shakka cikin lokaci ƙanƙani, farashin buƙatu za su ƙarƙarye, kuma mabuƙata musamman talakawa za su samu sauƙin rayuwa.

Mataimakin Sakataren ‘yan kasuwar, sai ya yi hamdala ganin yadda kasuwanci ke ta bunƙasa a jihar Gombe wanda a cewar shi, “duk waɗannan saboda yadda maigirma Gwamnanmu Alhaji Muhammad Inuwa Yahaya ya tinkari lamarin bunƙasa kasuwanci da wutar lantarki da tsaro da kuma haɗin kan al’umma suka kawo waɗannan ci gaban.”