Shugaban Kamfanin Binance ya maka EFCC da mashawarcin Tinubu a kotu

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Shugaban kamfanin Binance dake tsare a hannun hukumomin Nijeriya, Tigran Gambaryan ya maka Mashawarcin Shugaban Ƙasa Akan Harkokin Tsaro, Nuhu Ribadu da Hukumar EFCC mai yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin ƙasa zagon ƙasa a kotu bisa zarginsu da tauye masa haƙƙoƙinsa na bil adama.

A ƙarar da ya shigar, Gambaryan ya nemi kotu ta ayyana tsare shi da qwace masa takardun tafiye-tafiyen a matsayin laifin da ya sava sashe na 35 ƙaramin sashe (1) da na (4) na kundin tsarin mulkin na shekarar 1999.

Ya buƙaci kotun da ta umarci ofishin mashawarcin shugaban ƙasa akan harkokin tsaro da Hukumar EFCC su sake shi tare da dawo masa da takardun tafiye-tafiyensa nan take.

Gambaryan ya kuma buqaci kotun ta waɗanda ake ƙarar da wakilansu daga cigaba da tsare shi game da wani bincike ko buqata data shafi kamfanin Binance.

Haka kuma ya buƙaci kotun ta umarci waɗanda ake ƙarar su nemi gafararsa a bainar jama’a.

Gambaryan ya tabbatar da cewar ya zo Nijeriya ne tare da abokin aikinsa Nadeem Anjarwalla wanda ya tsere, domin mutunta gayyatar mashawarcin shugaban Nijeriya akan harkokin tsaro da Hukumar EFCC da nufin tattaunawa akan ayyukan kamfanin Binance a Nijeriya.

Ya ci gaba da cewar bai aikata wani laifi ba yayin ganawar, kuma ba’a shaida masa a rubuce wani laifi da ya tava aikatawa a Nijeriya a matsayinsa na mutum a kowane lokaci.

Gambaryan ya ƙara da cewar “dalili ɗaya tilo da ya sa ake tsare da shi ne gwamnati na neman bayanai daga Binance kuma tana da buƙatu game da kamfanin”, inda ya ƙara da cewar abokin aikinsa Nadeem Anjarwalla ma ya shigar da makamanciyar wannan ƙara.

A yayin zaman kotun da ya gudana ranar alhamis, Babban Lauyan Nijeriya T.J Krukrubo ne ya tsayawa masu ƙara a yayin da ɓangaren waɗanda ake qarar bai samu wakilcin kowa ba.

Krukrubo ya shaida wa kotun cewar an kaiwa ɓangaren waɗanda ake qara sammaci kwanaki 2 da suka gabata.

Jim kaɗan bayan hakan Krukrubo ya sanar da kotun cewar ya janye daga tsayawa Anjarwalla wanda ya tsere.

Saidai bai bada dalilansa na janyewar ba.

Alƙalin kotun, Mai Shari’a Inyang Ekwo, ya cage sauraran ƙarar zuwa ranar 8 ga watan Afrilu mai kamawa.