Gwamnan Kaduna ya ɗauki nauyin karatun ɗaliban Kuriga

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani, ya yi alƙawarin bai wa ɗaliban Kuriga 137 da aka kuvutar daga hannun ’yan bindiga tallafin karatu.

Gwamnan ya ce gidauniyarsa ta Uba Sani za ta gyara makarantun Kuriga domin bai wa yara a garin damar samun ingantaccen ilimi.

Gwamnan ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi ga ɗaliban da suka kuvuta daga hannun ‘yan bindiga a gidan gwamnatin jihar a ranar Alhamis.

Sani, ya ce bayan sako ɗaliban, gwamnatin jihar ta ɗauki masana ilimin halayyar ɗan adam aiki waɗanda suka shafe lokaci suna tattaunawa da ɗaliban don tabbatar da lafiyarsu.

Sai dai ya bayyana cewar ɗaya daga cikin malaman da aka sace, mai suna Malam Abubakar ya rasa ransa sakamakon matsalar rashin lafiya.

Gwamnan ya ce gwamnatin jihar za ta ɗauki nauyin karatun ’ya’yan malamin da ya rasu, tare da bai wa iyalansa kyautar Naira miliyan 10.

Sani ya ce, “Jiya iyayen ɗaliban sun zo nan, sun haɗu da yaran, kowa ya yi murna. Ina so na yaba wa yaran. Sun yi haƙuri da mu. Sun kuma fahimci halin da suka tsinci kansu a ciki.

“Lokacin da suka dawo, mun fahimci wasu na cikin matsanancin hali. Wannan shi ne dalilin da ya sa muka ɗauko masana ilimin halayyar ɗan adam, waɗanda suka ba su shawarwari. Na yi farin ciki kamar yadda yaran suka yi farin ciki.

“Kwana biyu da kuɓutarsu, sun nuna ba sa son komawa gida, sun so zama da ni a nan na tsawon mako biyu. Amma na sanar da su cewar ba zai yiwu ba dole su koma gida. Iyayensu na muradin ganin su bayan shafe kimanin kwana 17 a hannun ‘yan bindiga.”

Gwamnan ya ƙara da cewa, “Na kuma bayar da umarnin yin gyare-gyare a garin da kuma makarantunsu, domin Kuriga na ɗaya daga cikin yankuna mafi zaman lafiya a Kaduna.”

Gwamnatin Tarayya, ta musanta raɗe-raɗin da ake na cewar an biya kuɗin fansa domin sako ɗaliban.