Adadin marasa aikin yi a Nijeriya ya ragu zuwa kashi 4.3 a rubu’i biyu na 2024

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Hukumar ƙididdiga ta ƙasa (NBS) ta ce, adadin marasa aikin yi a Nijeriya ya ragu zuwa kashi 4.3 a rubu’i biyu na shekarar 2024.

Ofishin ya bayyana haka ne a cikin rahotonta na NLFS na kashi na biyu na shakrar 2024 da aka fitar ranar Litinin.

Adadin rashin aikin yi ya ragu zuwa kashi 4.3 a cikin rubu’i biyu daga kashi 5.3 a cikin rubu’i ɗaya na 2024.

Hukumar ta NBS ta ayyana rashin aikin yi a matsayin ƙaruwar ma’aikatu (samuwar aikin yi da ma’aikatu), waɗanda ba su da aikin yi suna yawan samun aiki.

“Rashin aikin yi na kwata na biyu na 2024 ya kasance da kashi 4.3, yana nuna ƙaruwar kashi 0.1 idan aka kwatanta da daidai wannan lokacin a bara,” inji rahoton.

“Rashin aikin yi a tsakanin maza ya kai kashi 3.4% da 5.1 a tsakanin mata.

“A wurin zama, yawan marasa aikin yi ya kai kashi 5.2% a birane da kashi 2.8% a yankunan karkara. Adadin rashin aikin yi na matasa ya kasance 6.5% a cikin kwata na biyu na 2024, yana nuna raguwa daga 8.4% a cikin kwata na ɗaya na 2024.”

Dangane da samun ilimi, rahoton ya ce adadin marasa aikin yi a tsakanin masu karatun gaba da sakandare ya kai kashi 4.8 bisa ɗari; Kashi 8.5 cikin 100 na masu karatun sakandare, kashi 5.8 na masu karatun sakandare, da kashi 2.8 na masu karatun firamare a ƙ2 2024.