Sakamakon cire tallafin mai: Adadin fetur da ake amfani da shi a Nijeriya ya ragu da lita biliyan guda – Idris

Daga BASHIR ISAH

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan ‘Yan Ƙasa, Muhammad Idris, ya bayyana cewa, adadin man fetur da ake amfani da shi a Nijeriya ya ragu da lita biliyan ɗaya, kwatankwacin kashi 53 na adadin man da ake amfani da shi gabanin cire tallafin mai.

A cewarsa, hakan ya faru ne sakamakon tallafin fetur da gwamanti ta cire a watan Mayun Bara.

Ya bayyana haka ne a wajen buɗe-baki tare da ‘yan jarida da aka shirya kwanan nan a Kano.

Idris ya ce, la’akari da yawan raguwar amfani da fetur da aka gani, hakan na nuni da yadda a baya ake fasa-ƙwaurin man zuwa ƙetare don amfanin waɗanda ba sa biyan ƙasar harajin komai.

Ya jaddada cewa, lallai cire tallafin man ya zama wajibi saboda waɗanda ba sa biyan Nijeriya haraji su suka fi cin moriyar man bisa ga ‘yan ƙasa.

Ta bakinsa, “Adadin fetur da ake amfani da shi a ƙasa ya ragu da kimanin kashi 53%, ma’ana, litar mai sama da biliyan ɗaya da ake amfani da shi gabanin cire tallafin mai ya tafi.

“Tambayar da ya kamata kowa ya yi wa kansa ita ce, ina man ke tafiya a wancan lokaci? Me ya sa a lokaci guda amfani da man ya ragu da kusan kashi 53?

“Wannan na nufin ana ficewa da man ta kan iyaka ne don amfanin waɗanda ba sa bai wa Nijeriya harajin komai,” in ji Ministan.