Sojoji sun kashe ‘yan bindiga 106 a mako guda — DHQ

*Ana ci gaba da farautar waɗanda suka kashe sojoji 18 a Delta

Daga BASHIR ISAH

Babban Ofishin Tsaro (DHQ) da ke Abuja ya ce ba zai yi ƙasa a gwiwa ba wajen farauto ɓata-garin da suka kashe sojoji a Jihar Delta.

Mai magana da yawun rundunar, Manjo-Janar Edward Buba ne ya bayyana haka a ranar Juma’a.

Ya ce faɗi-tashin da sojoji ke ci gaba da yi na yaƙi da ta’addancin, suna yi ne don amfanin ƙasa.

A cewarsa, ”A ci gaba da ayyukan yaƙi da matsalolin tsaro sojoji sun ceto mutane da dama waɗanda aka yi garkuwa da su tare da miƙa su ga ‘yan uwansu.

“Haka nan, sun yi nasarar tarwatsa ayyukan ‘yan ta’adda a sassa daban-daban wanda hakan ya gurgunta ɓatagarin wajen hana su aiwatar da harkokinsu,” in ji shi.

Ya ce sakamakon ayyukan sojojin a sassa daban-daban na ƙasa a cikin wannan mako mai ƙarewa, sun samu nasarar kashe ‘yan ta’adda 106, sannan sun kama 103.

Kazalika, ya ce an damƙe ɓarayin mai 22, yayin da an ceto mutum 96 da aka yi garkuwa da su da dai sauransu.