10
Jun
Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU Aisha Adam Hussaini wacce a fagen rubutu aka fi sani da Ameera Adam, ita ce Gwarzuwar Gasar Hikayata ta BBC Hausa ta shekarar 2023. Marubuciyar labaran hikayoyi da almara, wacce Allah Ya yi wa baiwar sarƙafa labari cikin hikima da basira, kai ka ce a zamanin Barbushe take ko cikin Daular Ifiritai. Ƴar baiwa ce ta nunawa a fadar Sarki, domin kuwa babu wata gasar marubuta adabi da ake shiryawa wacce in Aisha ta shiga ba ta samun nasara, don haka ne ma nasarar ta a Gasar Hikayata ba ta zo wa mutane da dama a…
