ukarofi

11000 Posts
Majalisar Tarayya zata karɓi ƙudurin dokar sabon mafi ƙarancin albashi nan ba da jimawa ba- Tinubu

Majalisar Tarayya zata karɓi ƙudurin dokar sabon mafi ƙarancin albashi nan ba da jimawa ba- Tinubu

Shugaba Tinubu ya ba da tabbacin cewa nan bada jimawa ba zai tura ƙudurin mafi ƙarancin Albashi zuwa Majalisar Tarayya. Ya faɗi haka ne a yayin jawabin sa na ranar dimukraɗiya a ranar 12 ga watan Yuni. " a cikin mutuntawa tare da ƙungiyoyin Ƙwadago, mun tattauna a kan sabon tsarin albashi mafi ƙaranci. Nan ba da jimawa ba zamu aika da ƙudurin zuwa majalisa domin ya zama doka na shekara biyar ko ƙarancin haka" Ya ƙara da cewa babu ko ɗaya cikin jagororin Ƙungiyar Ƙwadago da aka tsangwama ko aka kama a dalilin yajin aikin da suka yi ranar…
Read More
Ƴan bindiga sun harbe yan sanda biyu da farar hula ɗaya a Jihar Imo

Ƴan bindiga sun harbe yan sanda biyu da farar hula ɗaya a Jihar Imo

Wasu yan bindiga sun harbe yan sanda biyu da farar hula daya a Akabu, ƙaramar hukumar Ikedurun Jihar Imo a safiyar Talata. Wasu shaidun gani da ido sun shaida cewa harin ya faru ne a wani shinge dake kan titin Owerri-Okigwe-Enugu.Yan bindigar waɗanda ke tuƙa mota ƙirar siena sun shammaci yan sanda ne daga baya kuma suka tsere bayan sun gama. Mai magana da yawun yan sandan Jihar Imo, ASP Henry Okoye ya tabbatar da faruwar wannan al'amari.
Read More
Ana zargin Babban Sakataren Ma’aikatar Ƙasashen waje da cin zarafin mata

Ana zargin Babban Sakataren Ma’aikatar Ƙasashen waje da cin zarafin mata

A wani jawabi mai kiɗimarwa, Ministan harkokin ƙasashen waje, Ambasada Yusuf Maitama Tuggar ya rubuta takardar ƙorafi zuwa ga shugabar ma'aikatan Najeriya, Dr Folasade Yemi-Edan, a kan zargin Babban Sakataren ma'aikatar, Ambasada Ibrahim Adanmu Lamuda da cin zarafin wata matar aure ma'aikaciyarsa, Mrs Simisola Fajemirokun. Ƙorafin yana ƙunshe ne a wata wasiƙa da News Point Nigeria ta samu damar gani, wanda ke ɗauke da kwanan wata 27 ga watan Mayu, 2024, mai taken " ƘORAFI DANGANE DA CIN ZARAFIN MRS SIMISOLA FAJEMIROKUN AJAYA DA AMBASADA IBRAHIM ADAMU LAMUWA (BABBAN SAKATAREN MA'AITAKAR HARKOKIN KASASHEN WAJE) YA YI" Wasiƙar, wacce take ɗauke…
Read More
Tinubu zai yi wa ‘yan Nijeriya jawabi Ranar Dimukraɗiyya

Tinubu zai yi wa ‘yan Nijeriya jawabi Ranar Dimukraɗiyya

Shugaba Tinubu zai yi ma yan Najeriya Jawabi ranar dimukraɗiya da misalin 7am ranar Laraba. Mai baiwa Shugaban ƙasar shawara Ajuri Ngelale ne ya sanar da hakan a wani bayani da ya fitar ranar Talata a Abuja. Wani sashen bayanin yana cewa " Gidajen talabijin da rediyo da duk wasu kafofin yaɗa labarai su nemi jawabin ta hanyar gidan talabijin na ƙasa wato NTA da kuma FRCN"
Read More
An tabbatar da mutuwar Mataimakin  Shugaban Ƙasar Malawi

An tabbatar da mutuwar Mataimakin Shugaban Ƙasar Malawi

Shugaban ƙasar Malawi Lazarus Chakwera ya faɗa ranar Talata cewa ba a samu wanda ya rayu ba a cikin jirgin da ke ɗauke da mataimakinsa Saulos Chilima da kuma wasu mutum tara lokacin da jirgin su ya faɗi a wani daji. Masu neman jirgin sun sami nasarar gano ɓarguzan jirgin lokacin da a ka nemi jirgin ba a gani ba. Jirgin an neme shi ba a ganshi ba jiya Litinin lokaci da yakamata ya sauka a wani gari Mzuzu da ke arewacin ƙasar amma ya gaza hakan sabida yanayi marar kyau. Wasu hotuna da gidan Jarida na AfP ya fitar…
Read More
An yi garkuwa da fasinjoji a hanyar Maiduguri zuwa Kano

An yi garkuwa da fasinjoji a hanyar Maiduguri zuwa Kano

Wasu Mahara da ake zargin yan boko haram ne sun yi garkuwa da fasinjoji da dama a kan hanyar Maiduguri zuwa kano. Maharan sun kai hari ne tsakanin garin Kuturu da ƙauyen Mannanari wanda ke kusa da ƙauyen Auno. Sun kai harin ne da yammacin litinin wajen karfe 5:50pm. Al'amarin ya tsayar da zirga zirga kan titin na tsawon lokaci wanda ya tursasa wasu komawa garin Banisheik da Auno. Wasu Mazauna Ƙauyukan sun bada labarin yadda masu motocin haya suka fake a garuruwansu domin jiran lokacin da sojoji zasu buɗe hanyar.
Read More
Mafi ƙarancin albashi: Dalilan da ya sa ba za mu koma yajin aiki ba- Ƙungiyar Ƙwadago

Mafi ƙarancin albashi: Dalilan da ya sa ba za mu koma yajin aiki ba- Ƙungiyar Ƙwadago

Ƙungiyar Ƙwadago tace ba za ta koma yajin aiki ba a ranar 11 ga watan Yuni kan tattaunawar ta da gwamnatin tarayya a kan mafi ƙarancin albashi. Shugaban ƙungiyar Ƙwadagon, Joe Ajaero ne ya sanar da haka a wani taron ƙasa da ƙasa a birnin Geneva, Switzerland. Ajaero ya jaddada cewa, alƙaluman suna gaban shugaban ƙasa, don haka ba za su iya tafiya yajin aiki yanzu ba. "Muna jiran mu ji me shugaban ƙasa zai ce sannan mu zauna taron masu ruwa da tsaki a ƙungiyar Ƙwadagon don sanin menene kuma zamuyi a gaba." Sannan Ajaero ya soki wasu gwamnoni…
Read More
Gwamnatin Tarayya ta sanar da 12 ga Yuni a matsayin hutun Ranar Dimukraɗiyya

Gwamnatin Tarayya ta sanar da 12 ga Yuni a matsayin hutun Ranar Dimukraɗiyya

Gwamnatin Tarayya ta sanar da 12 ga Yuni a matsayin hutun Ranar DimukraɗiyyaMinistan harkokin cikin gida, Hon.Dr Olubunmi Tunji Ojo ya fitar da sanarwa yana mai cewa " yayin da muke murnar zagoyowar ranar dimukraɗiya a tarihin ƙasar mu. Yana da kyau muyi waiwaye domin ganin yadda magabatan mu suka jajirce don ganin Najeriya ta zama tsintsiya maɗaurinki ɗaya.Ministan ya ƙara da cewa, Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu yana iya bakin ƙoƙarinsa don ganin kawo canji ga tattalin arziki da tsaron kasa.Ministan yayi kira ga yan Najeriya da abokan ta da su yi alfahari da ita ganin yadda ta cigaba…
Read More
Yan Ta’adda sun kai hari a sansanin sojoji da ke jihar Niger

Yan Ta’adda sun kai hari a sansanin sojoji da ke jihar Niger

Aƙalla sojoji biyu ne suka samu raunuka lokacin da wasu yan ta'adda suka kai wani hari a sansanin sojoji da ke Tegina, karamar hukumar Rafi jihar Niger An kashe dan ta'adda ɗaya yayin musayar wuta da sojojin. Wasu majiya sun bayyana cewa yan ta'addan na shirin tsallakawa ne daga ƙaramar hukumar Wushishi zuwa Mashegu lokacin da suka kai harin. Alhaji Ayyuba Usman Katako, shugaban ƙaramar hukumar Rafi, ya tabbatar da faruwar al'amarin in da yace sojojin da suka samu raunuka na Asibitin IBB da ke Minna domin samun kulawa.
Read More
Shekara Guda: Wacce rawa Shettima ke takawa a Gwamnatin Tinubu?

Shekara Guda: Wacce rawa Shettima ke takawa a Gwamnatin Tinubu?

Daga STANLEY NKWOCHA Shekara  guda kenan da rantsar da Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu (GCFR), wato a ranar 29 ga Mayu, 2023, kuma nan take ya ɗauki alwashin samar da sauye-sauyen da za su bayar da sakamakon da zai sauya akalar harkokin mulki a Najeriya baki ɗaya. Kuma mun gani a ƙasa, domin a shekara guda na mulkinsa ya qaddamar da ƙudurorinsa ƙarƙashin taken ajandodi 8 na Sabunta-Fata, wanda suka tafi kafaɗa-da-kafaɗa da alƙawuran da ya ɗauka a lokutan yaƙin neman zaɓensa. Wato abin nan da ake kira aiki da cikawa. Duk da abu ne mawuyaci a yi wa gwamnatin…
Read More