Ƴan bindiga sun harbe yan sanda biyu da farar hula ɗaya a Jihar Imo

Spread the love

Wasu yan bindiga sun harbe yan sanda biyu da farar hula daya a Akabu, ƙaramar hukumar Ikedurun Jihar Imo a safiyar Talata.

Wasu shaidun gani da ido sun shaida cewa harin ya faru ne a wani shinge dake kan titin Owerri-Okigwe-Enugu.
Yan bindigar waɗanda ke tuƙa mota ƙirar siena sun shammaci yan sanda ne daga baya kuma suka tsere bayan sun gama.

Mai magana da yawun yan sandan Jihar Imo, ASP Henry Okoye ya tabbatar da faruwar wannan al’amari.

By ukarofi