Yan Ta’adda sun kai hari a sansanin sojoji da ke jihar Niger

Aƙalla sojoji biyu ne suka samu raunuka lokacin da wasu yan ta’adda suka kai wani hari a sansanin sojoji da ke Tegina, karamar hukumar Rafi jihar Niger

An kashe dan ta’adda ɗaya yayin musayar wuta da sojojin. Wasu majiya sun bayyana cewa yan ta’addan na shirin tsallakawa ne daga ƙaramar hukumar Wushishi zuwa Mashegu lokacin da suka kai harin.

Alhaji Ayyuba Usman Katako, shugaban ƙaramar hukumar Rafi, ya tabbatar da faruwar al’amarin in da yace sojojin da suka samu raunuka na Asibitin IBB da ke Minna domin samun kulawa.

Leave a Reply