Shekara Guda: Wacce rawa Shettima ke takawa a Gwamnatin Tinubu?

Daga STANLEY NKWOCHA

Shekara  guda kenan da rantsar da Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu (GCFR), wato a ranar 29 ga Mayu, 2023, kuma nan take ya ɗauki alwashin samar da sauye-sauyen da za su bayar da sakamakon da zai sauya akalar harkokin mulki a Najeriya baki ɗaya.

Kuma mun gani a ƙasa, domin a shekara guda na mulkinsa ya qaddamar da ƙudurorinsa ƙarƙashin taken ajandodi 8 na Sabunta-Fata, wanda suka tafi kafaɗa-da-kafaɗa da alƙawuran da ya ɗauka a lokutan yaƙin neman zaɓensa. Wato abin nan da ake kira aiki da cikawa.

Duk da abu ne mawuyaci a yi wa gwamnatin da ta gaji tarin matsaloli na shekara da shekaru alƙalanci a shekararta ta farko, amma duk da haka za a iya ɗora manufofin da gwamnatin ta mai da hankali a kansu bisa sikeli don hasaso nasara ko akasinta a turbar da ta hau. Nan ma amsar ita ce sambarka!

Masu magana kan ce ba a gini bisa tubalin toka. Wannan ita ce kalmar da ta dace da ƙiyasin abinda Shugaba Tinubu ya yi a shekara ɗaya na mulkinsa ƙarƙashin Ajandar Sabunta Fata Nagari, a matsayinsa na maginin Sabuwar Najeriya ya san ɗora gini a kan rusasshen harshashi ba zai taba samar da ɗa mai ido ba, don haka ya zama dole ya baje turakun tokar da aka shimfiɗa Najeriya a kai ya shimfiɗa mata nagartaccen tubali.

Ba fa kan mu farau ba, kusan duk faɗin duniya, gwamnatoci kan ci karo da irin wannan yanayi a shekarun mulkinsu na farko. Abu na farko da ya wajaba ga ko wace sabuwar gwamnati shine kafa sabuwar majalisar ministoci, da zaɓo nagartattun mutane da za su riqe madafun iko a ɓangarorin zartarwa. Sai abu na biyu, wanda shine fayyacewa tare da ɓullo da tsare-tsare na manufofin da za su tafi sau da kafa da abubuwan da suka alqawarta wa al’ummar ƙasa. Abu na uku, shine kafa tsarin shugabanci bisa doron manufofin da za su dace da manufofin takwarorinsu na ƙasashen waje

Tun bayan samin ’yancin kan Najeriya a shekarar 1960, ƙasar ke taka rawa sosai a harkokin Afirka da ma duniya baki ɗaya. Hakan ya sa su ma qasashen duniya na sanya manufofi da tsare-tsaren sabbin gwamnatocin Najeriya a faifai a matsayinta na giwar Afirka domin tantance yadda za ta aiwatar da mulkinta, kamar yadda su ma al`ummar ƙasa kan sanya idanu kan manufofin ƙasashen waje da kuma muradun sabbin shugabannin qasar.

A irin wannan yanayi, ba sabon abu ba ne masu taimaka wa shugaban ƙasa su yi gudun-wuce-sa’a ta bayan fage don tabbatar da kwazon su a wani aiki ba

Sabanin zarge-zargen da ke shawagi a wasu kafofi cewa wai! An yi watsi da mataimakin shugaban qasar, na san idan da adalci su kansu masu kumfar bakin shaidu ne kan cewa mataimakin shugaban ƙasa Sanata Kashim Shettima ya taka rawa a muhimman wuraren da ake bukatarsa. Amma idan sun kasa bayar da shaidar ni zan bigi kirji na tabbatar da wannan ikirarin nawa

Cikin ruwan sanyi VP Kashim Shettima yake samin damar jagorantar manyan aiyukan da a baya wadanda suka taa xana kujerar mataimakan shugaban qasa kan same su ne a  mafarki ko kuma bayan sun sha wahala.

A yayin da Shugaba Tinubu ke mayar da hankali kacokan kan harkokin gudanar da Mulki, mataimakinsa na taimaka masa a bangaren da ya fi kwarewa a fannin farfado da tattalin arzikin Najeriya na gama-gari a matsayinsa na gogaggen masanin tattalin arziki da noma, da sabbin dabarun habaka tattalin arzikin duniya na karni na 21

 A shekararsu ta farko kan karagar mulki, Shugaba Tinubu da VP Shettima sun dukufa wajen tabbatar da mulkin Najeriya, inda suka fuskanci matsaloli da dama musamman a bangaren tattalin arziki, tsaro da walwalar ‘yan qasa. Ajandodi 8 na gwamnatin Tinubu sun samar da tsayayyen tsari ga manufofi shirye-shiryen gwamnatin, tare da mai da hankali kan samar da ayyukan yi, bunqasar tattalin arziki, samar da abinci, kawar da talauci, samun jari, bin doka da oda, yaki da cin hanci da rashawa, da ci gab ana bai daya.

Ko shakka babu, Shugaba Tinubu yana da cikakken masaniya kan kwarewar Kashim Shettima a bangaren jagoranci, shiyasa ma ya zabe shi a matsayin abokin takararsa, kuma ba ya da haufi cewa Kashim ba zai yi qasa a gwiwa ba a matsayinsa dan gani-kashenin jigo a siyasar Arewa mai mara wa shugaban baya.

Kamar yadda aka zata, mataimaki kuma amintaccen aminin shugaban qasa, ya taimaka wajen aiwatar da manyan sauye-sauyen da gwamnatin Sabunta Fata-na gari ta taso a gaba, tare da daukar matsaya da zartas da hukumci a kan batutuwa masu sarkakiya da suka shafi gudanar da  mulkin qasa, wannan kenan, baya da manyan taruka da shi mataimakin shugaban ƙasar ke jagoranta a madadin me gidansa a mafi yawan lokuta domin sake farfado da  ruguzajjen tattalin arzikin da suka gada.

Sau da yawa shuwagannin biyu kan yi amfani da kwarewarsu a jagoranci da siyasa don samar da sabon tsarin jagoranci.

Baki dayan masu lura da al’amuran yau da kullum sun yi amannar cewa mataimakin shugaban qasa jajirtacce ne kuma ya iya sadaukar da kai wajen tafiyar da ayyuka.

Shugaban da mataimakinsa sun hada karfi da karfe wajen zame wa Najeriya jirgin Annabi Nuhu (AS) don ceto ta daga nutsewa a tekun matsalolin da suka gada.

Kada na cika ku da surutu, bari na jero wasu daga cikin matakai da ginshikan da suka kafa ya zuwa yanzu:

1. A Bangaren Huldar Diflomasiyar Duniya Da Zuba Jari Na ƙasashen Waje

Bayan hawansu mulki, shugaba Tinubu da mataimakinsa Shettima sun fara gudanar da manyan ayyuka da suka shafi ƙasa da ƙasa, inda aka yanke shawarwari masu muhimmanci da suka shafi Najeriya da nahiyar Afirka, kuma a mafi yawan lokuta shugaban kan nuna kwarin gwiwa kan  Shettima na iya wakiltar qasar da kyau a ko ina a fadin duniya, ba akan al`amurran da suka shafi matakan da gwamnati ta dauka kaɗai ba har ma da manyan al’amurran da suka hada da  muhimman tarurrukan a ciki da wajen qasa.

Da kwarewar shuwagabannin ta iya tallata haja ne suka yi nasarar dawo da kwarin gwiwar masu zuba jari a kasuwannin Najeriya a kusan kowane taron qasa da qasa suka halarta.

A watan Nuwamban shekarar da ta gabata ne mataimakin shugaban qasa Shettima ya bi sahun shugabannin qasashen duniya kimanin 130 a wajen taron BRI karo na 3 da aka yi a ƙasar Sin, inda ya ja hankalin masu zuba jari daga qasashen waje kan samun saukin harkokin kasuwanci a Najeriya, inda ya bayyana musu cewa, Nijeriyar yau amintacciyar qasa ce ga masu zuba jari. Daga qasar Sin kai tsaye Shettima ya wuce ƙasar Amurka don halartar taron tattaunawar ƙasa da ƙasa na Norman Borlaug don samar da kyautar abinci ta duniya wanda bankin raya qasashen Afirka (AfDB) ya shirya a jihar Iowa, A nan ma mataimakin ya jawo hankulan masu zuba jari tare da shaida musu alkawuran da shugaba Tinubu ya dauka don samar da abinci da habaka tattalin arziki a Najeriya. Daya daga cikin ganimar da VP din ya samo a wannan balugoro ita ce rubanya ayyukan bunqasa noma na Bankin Raya Afirka (AfDB) a Najeriya inda ya tashi daga dala miliyan 500 zuwa sama da dala biliyan guda.

Bayan watanni biyu da hawansa mulki, mataimakin shugaban qasa Shettima ya wakilci shugaba Tinubu a wasu manyan tarukan qasa da qasa guda har guda biyu a qasashen Roma, Italiya da St. Petersburg inda ya bi sahun sauran shuwagannin duniya a taron farko na (STM) Kazalika ya jagoranci wani babban taro mai taken ‘Innovative Financing for Food System Change: the case of Nigeria’.wato taron kirkiro da sabbin dabarun sauya tsarin tallafa wa samar da abinci

Haka ma a ziyararsa a qasar Rasha don halartar taro tsakanin Rasha da Nahiyar Afirka karo na 2, Shettima ya bi ayarin sauran shugabannin siyasa da ‘yan kasuwa a taron tattalin arziki da jin kai na Rasha da Afirka wanda aka mayar da hankali kan dabarun karfafa dangantakar da ke tsakanin Rasha da nahiyar Afirka da dai sauransu.

VP Shettima ya kuma zauna da manyan jami’an gwamnatin Rasha da shugabannin ‘yan kasuwa a ƙasashen biyu, inda suka tattauna kan huldar dangantakar Rasha da Najeriya.  

Kwanan nan, Sanata Shettima ya tafi birnin Nairobin qasar Kenya, inda ya wakilci shugaba Tinubu a wajen taron shugabannin qasashe masu tasowa(IDA 21).

Wasu daga cikin nasarorinda suka biyo bayan wadannan tafiye-tafiyen sun hada da shawarar da wani kamfanin Amurka, John Deere, ya yanke na zuba jari a fannin noma a Najeriya, inda kamfanin ya ce zai fara da kafa kamfanin hada motocin noma a qasar, sai kuma sabon alqawarin da qasar Sin ta dauka na kammala aikin da aka dade ana dakonsa wato aikin layin dogo daga Legas zuwa Ibadan da Abuja-Kano da Port-Harcourt-Maiduguri.

Akwai kuma yarjejeniyar da aka rattaba wa hannu da za ta farauto wa Najeriya sama da dala biliyan 2, zuwa 4. Hakan na nuna irin yawan hannayen jari na kai-tsaye da aka samu a dunkule daga qasashen ketare zuwa ga muhimman bangarori da suka shafi bunqasa fasaha, motoci da sauran ababen more rayuwa.

Wadannan yarjejeniyoyin sun hada da kulla kwakkwarar dangantaka tsakanin hukumar  (NASENI) da kamfanonin ƙasar Sin daban-daban, da kuma alkawurran samar da wutar lantarki da fasahar dijital don tinkarar kalubalen gurbataccen makamashi a Najeriya da bunqasa sabbin fasahohin zamani masu matukar muhimmanci wajen dorewar ci gaba na  dindindin. .

A yanzu qasar mu na iya Alfahari da bugun kirji da damammaki masu yawa na bunqasar tattalin arziki da suka hada da hanyoyin inganta samar da wutar lantarki, tsaro, samar da man fetur da iskar gas, sufuri, kamun kifi, yawon bude ido da ma sauran harkokin kasuwanci da zuba jari na ƙasa da ƙasa. Wannan ya nuna ƙarara yadda abokan huldar qasa da qasa ke qara samin kwarin gwiwa kan karfin tattalin arzikin Najeriya daga gwamnatin Shugaba Tinubu da Shattima.

2. A bangaren NEC

Idan muka komo gida Najeriya ma ba a bar Sanata Shettima a baya ba, domin a matsayinsa na shugaban Hukumar Tattalin Arzikin Qasa ta (NEC), an samar da sabbin shirye-shirye da ayyuka da dama na gwamnatin tarayya a qarqashin ofishin mataimakin shugaban qasar.

Ga wasu Misalai, NEC ta amince da aiwatar da shirin zuba jari na dala miliyan v17.7 a jihohi 3v da babban birnin tarayya kan fasahar sadarwa ta zamani da qirqirarrun hanyoyin saye da sayarwa wato (i-DICE)  domin samar da ayyukan yi a bangaren kere-kere da fasaha ta hanyar horas da matasa sama da miliyan 1.2 kai-tsaye kan fasahar ICT da ma wasu aiyukan da ba na kai-tsaye ba da suka kai milyan 5.v a fadin qasar.

A bangaren shawo kan matsalar karancin abinci da na tattalin arziki a  ƙasa kuwa, hukumar NEC ta yunkura don aikin samar da takin zamani ga manoma, tare da kafa wata runduna da aka yi wa taken Agro-Rangers domin samar da tsaro a gonaki da kuma tabbatar da ana amfani da sabbin dabarun noman zamani.

Har ila yau, Hukumar ta NEC ce ta jagoranci samar da yankin sarrafa amfanin gona na musamman na gwamnatin tarayya da ake kira (SAPZ) a takaice domin inganta harkar noma a Najeriya tare da rage dogaro da shigo da abinci daga qasashen qetare.

Majalisar ta NEC qarqashin mataimakin shugaban qasa ta samar da taswirar yadda za a shawo kan matsalolin ambaliyar ruwa da samar da ingantaccen tsarin bayar da agaji mai samin haɗin gwiwar qungiyar gwamnoni ta Najeriya.

3. Pulaku Initiative

Tukuru ofishin mataimakin shugaban qasa ke aikin sanya ido kan shirin Pulaku, wani sabon tsari na qashin kai da gwamnatin Tinubu ta qirqiro domin magance musabbabin matsalolin da suka addabi yankunan Arewa wanda suka haxa da rikici tsakanin manoma da makiyaya, da ‘yan tada qayar baya, da ‘yan fashin daji da tsabar fatara.

A qarqashin wannan shiri za a gina sama da gidaje 1,000 da asibitoci da shaguna a kowace jaha daga jahohin Arewa maso Yamma domin biyan diyya ga wanda rikicin ya rutsa da su

4. Shirin Haskaka Nigeria.

A watan Fabrairun wannan shekara, mataimakin shugaban qasa Shettima ya qaddamar da shirin Light Up South East Initiative, don hanzarta samar da wutar lantarki ga rukunin masana’antu a yankin Kudu maso Gabashin Najeriya, shi dai wannan shiri na haxin gwiwa ne tsakanin Kamfanin Neja Delta Power Holding Company Limited (NDPHC) da abokan hulxar sa.

A ita dai wannan rana, mataimakin shugaban ƙasar ya ƙaddamar da aikin samar da wutar lantarki mai karfin megawatt 181 a rukunin masana’antu na Osisioma da ke garin Abar  jihar Abia.

Kazalika Shettima tare da haɗ8n gwiwa da masu ruwa da tsaki da suka himmatu wajen samar da nasarar haskaka Najeriya, ya kaddamar da makamancin wannan  shiri na hasken lantarki a yankin Kudu maso Yammacin Najeriya, shi ma a rukunin masana’antu na Agbara a ranar 12 ga Oktoba, 2023, jihar Ogun,

5. Shirin Rarraba Ilimi

A watan Mayun bana ma, mataimakin shugaban qasar  ya je jihar Bauchi inda ya qaddamar da shiri mai dogon zango na bunqasa manyan makarantun gaba da sakandare (ASSEP). Daya daga cikin abubuwanda wannan shirin zai gudanar shine gyaran makarantu, da sabunta manhajojin koyarwa, da shigar da fasahohin zamani na gani da ido a fannin koyarwa.

Wannan shiri wanda zakaran gwajin dafinsa ke Arewa maso Gabas dai wani babban shiri ne na xinke varakar da ilimi ke fama da ita a qasar nan,

6. Shirin Sake Tsugunar Da Wadanda Rikici Ya Xaixaita

A ranar Litinin din da ta gabata ne mataimakin shugaban qasa Shettima ya qaddamar da wani shirin kan yadda Jihohi za su samar da hanyar magance matsalolin muhalli ga waxanda rikici ya raba da garuruwansu

A wajen qaddamarwar, mataimakin ya yi kira da a haxa hannu da qasashen duniya don magance matsalar gudun hijira a Najeriya.

Shi dai wannan shiri na daga cikin ajandar Sakatare Janar na majalisar xinkin Duniya kan samar da mafita ta dindindin ga matsalar matsugunai ga `Yan Gudun Hijira don samar musu da mafita mai ɗorewa, da hana sake b`arkewar  rikicin mai haddasa ƙauracewa muhalli, da kuma tabbatar da waxanda ke fuskantar ƙaura sun sami ingantaccen kariya da taimako.

Da yake kaddamar da shirin wanda ake aiwatarwa a jihohi huxu da suka haxa da Adamawa, Benue, Borno da Yobe, VP ya ce gwamnatin tarayya ta duƙufa wajen tabbatar da tsaro da jin daƙin ‘yan gudun hijira.

7. Sake Farfado da Kananan Kasuwanci

A wani mataki na tallafa wa masu kananan sana’o’i ta hanyar samar musu da dausayin ci gaba, shugaba Tinubu ya fara aikin kafa sana’o’i miliyan xaya a faxin Najeriya. A bisa haka ne mataimakin shugaban qasa Shettima ya qaddamar da dandalin Hab`aka kananan masana’antun MSME na qasa a garin Makurdi a jihar Benuwe wanda ya zama xigon xan-Ba a yunqurin  qarfafa wa qanana da matsakaitan ‘yan kasuwa gwiwa a fadin qasar nan. Dandalin na MSME, shine irinsa na farko a qarqashin gwamnatin Tinubu, da nufin qarfafa qanana da matsakaitan masana’antu (MSMEs) ta hanyar cire duk qananƙalubale da masu masana`antun ke fuskanta da samar musu da damammakin bukatunsu na kasuwanci. Samar da dandalin na MSMEs na da alaƙa da kokarin gwamnati na sauke nauyin Alqawarin da ta xauka kan sauƙaƙe hanya ga ƙananan ‘yan kasuwa.

Duk da jahar Benue ce ta fara qaddamar da dandalin MSME, ana shirin samar da ire-irensa a duk fadin qasar inda zai ratsa jihohin Ebonyi, Ogun, Delta, Kaduna, Borno, Katsina da kuma babban birnin tarayya Abuja a kashinsa na farko wanda ya gudana rabin shekarar 2024.

Kazalika a watan Maris, Sanata Shettima ya qaddamar da kashi na biyu na Shirin fadada kasuwar MSME din ta qasa a jihar Ogun inda aka miqa sabbin shaguna har 200 da aka gyara don amfanin ’yan kasuwa 400 a fitacciyar kasuwar Asero Adire da ke Abeokuta.

8. Magance Talauci Ta  Hanyar Samar Da Kudaden Shiga

A ci gaba da kokarin da gwamnatin Tinubu ke yi na fitar da ‘yan Najeriya daga qangin talauci, mataimakin shugaban qasa Shettima, a ranar 25 ga watan Afrilun bana, ya qaddamar da shirin gwamnatin tarayya na Aso Accord on Economic and Financial Inclusion. Wani shiri mai bangarori da dama da aka tsara domin samun damar shiga tsare-tsaren samun kuxaxen shiga a faxin Najeriya. Yarjejeniyar Aso ta samar da ingantaccen tsarin dimokaradiyya don samun damar samun kuxi, qarfafa wa ‘yan kasuwa gwiwa da samar da ci gaban tattalin arziki mai xorewa tun daga tushe. Shi dai wannan tsari ya zamo tamkar wani yekuwa ne don buxe kowace irin dama ga `yan Najeriya don cimma burin su na tattalin arziki wanda ke wakiltar babbar ajandar sabunta-fata ta gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan mayar da ƙasar  ga turbar tattalin arziki mai iya tattara  tiriliyan 1 na Dala nan da shekarar 2030 tare da yaƙi da talauci da rashin tsaro ta hanyar wadata mai bin doka.

Ta hanyar amfani da sauye-sauyen da sabbin dabaru a fannonin saka jari, Taswirar Aso Accord ta samar da hanyoyin cike manyan givin da ake bari na miliyoyin ‘yan Najeriya, musamman mata, matasa, mazauna karkara, da qananan ‘yan kasuwa, wajen qasa samin muhimman ayyukan samun qudaden lamuni, inshora, fansho, da wuraren ajiyar kuxi

9. Gina QasaTa Hanyar Abinci Mai Gina Jiki

A qarqashin qudirin gwamnatin Tinubu na samar da abinci mai gina jiki da rahusa, kwanan nan mataimakin shugaban qasa Shettima ya qaddamar da wani gagarumin shiri na inganta abinci mai gina jiki a fadin Najeriya, tare da yin kira ga Shugabannin addini da na gargajiya da su jagoranci wannan yunkuri a yankunansu.

A wajen babban taron tattaunawa kan abinci mai gina jiki da aka gudanar a fadar shugaban qasa,, VP Shettima ya jaddada cewa ba kawai a kan wadatar abinci ci gaban Najeriya ya ta’allaka ba,, har ma da samar da abinci mai gina jiki. Tattaunawar ta yini xaya mai taken, “Jagororin Addini A  Matsayin Masu Kayatar da Jikin Dan Adam Ta Hanyar Gina Jiki,” Majalisar Kula da Gina Jiki ta Qasa da Majalisar Dinkin Duniya da Bankin Duniya da ke Tallafa wa [ANRiN] Project ne suka shirya taron.

A qoqarin Kwamitin NEC qarqashin jagorancin mataimakin shugaban qasa da haxin gwiwar shuwagabannin addinai da ma wasu masu ruwa da tsaki, an dauki aniyar samar da fasalin daqile yunwa da rashin abinci mai gina jiki da qalubalen da ke tattare da su.

10. Ba Sani Ba Sabo Kan Noma

Bisa la’akari da varnar da aka tafka a wasu muhimman bangarori da suka haxa da noma na tsayin shekaru. Da hawa karagar mulkin Shugaba Tinubu, a shekarar da ta gabata, ya fara aiwatar da sauye-sauye masu tsauri don kawo gyara a fannin noma. Roko na farko da shugaban  ya yi shi ne ‘yan Najeriya su koma gona, domin da ruwan ciki ake Jan na rijiya.

Shugaba Tinubu bai yi qasa a gwiwa ba wajen kafa dokar ta-baci kan samar da abinci. A wani vangare na qoqarin da sabuwar gwamnatin ta yi na shawo kan hauhawar farashin kayan abinci bayan radadin da cire tallafin man fetur ya haifar shugaban ya kuma amince da shigar da duk wani abu da ya shafi sauqaqa samar da abinci da ruwa cikin rukunin farko na ababen more rayuwa, kuma ya sanya su cikin  aiyukan Majalisar Tsaron Qasa.

A fannin farfaxo da fannin bunqasayawan amfanin gona a gida da bunqasa tattalin arzikin qasar kuwa, shugaban ya bayyana wasu tsare-tsare da suka hada da faɗaɗa filayen noma zuwa hekta 500,000, da samar da rancen kuɗaxe masu qarancin ruwa ga manoma da zuba jari a fannin noman rani. Hakan ya biyo bayan sakin takin zamani da iri ga manoma da magidanta don rage radadin cire tallafin.  

A watan Maris ɗin bana ne ‘yan Najeriya suka fahimci dimbin amfanin da ke tattare da jarin da Tinubu ya zuba a bangaren noma a yayinda shugaban ya ƙaddamar da shirin samar da abinci da sarrafa kayan gona a Minna, babban birnin jihar Neja. Aikin wani shiri ne na gwamnatin jihar Neja mai niyyar amfani da manyan injinan noma da fasaha domin bunqasa amfanin gona a jihar.

A karon farko qarqashin gwamnatin Tinubu, Najeriya ta fara shaida wani sabon salo na  aiki tare tsakanin shugaban qasa da mataimakinsa. Misali, yayin da Shugaba Tinubu ke zaburar da gwamnatocin ƙasa baki daya wajen ganin sun shiga cikin tsarin hab`aka noma na gwamnatin tarayya, a kullun za ka ji VP Shettima na tabbatar da cewa  gwamnatinsu na da fatan zama a bar koyi.

A Shekarar bana, mataimakin shugaban ƙasar ya fitar da nasa tsarin ƙarfafa wa manoman ƙasar nan don cimma nasarar shirin samar da abinci da aikin noma na gwamnatin Tinubu. Shirin mai suna Kashim-Shettima Foundation’s Agricultural Empowerment Programme, wanda aka qaddamar a jihar Kaduna, ya nuna cewa an fara rabon taraktoci, da iri, da takin zamani, da magungunan kashe kwari, da sauran muhimman kayan noma ga manoman da za su amfana da noman shekarar 2024.

Bugu da qari, shirin ya kuma ba da damar samin tallafin qarfafa gwiwa ta hanyar bayar da N100,000 ga kowane daya daga cikin masu cin gajiyar shirin guda 50 a tsawon watanni 4 na lokutan shuka.

Haka zalika za a bai wa kungiyoyin manoman da suka kunshi manoma 50 kuxaxen fara aiki har Naira miliyan 30 domin kafa gonakin kasuwanci.

Salon shugabancin da Kashim Shettima ke son bari a matsayinsa na lamba biyu a Najeriya shi ne koyar da bautar ƙasa da sadaukar da kai, rikon amana, biyayya ga gwamnatin Tinubu.

A ko ina ka hadu da Kashim bashi da aiki sama da ya nuna nagartar maigidansa, wadannan halayen nasa da ma wasu na salon shugabancinsa sun sa ‘yan Najeriya da dama na kaunarsa da  ganinsa a matsayin cikakken mataimaki ga shugaban qasa.

Lallai idan aka ce a ci gaba da ninkaya a bayani kan nagarta da hankalin Kashim, Alkaluma  da yawa za su bushe ba tare da an kammala ba.

Haɗin kai da amincin da ake gani tsakanin shugabannin biyu na da ban sha’awa, domin duka mutanen biyu a cikin shekara ɗaya da kama mulkinsu sun nuna kamanceceniya wajen hidimta wa ƙasa da sadaukarwa da kuma gaskiya a cikin shugabanci.  Kuma Mataimakin shugaban ƙasar yayi nasarar cusa aƙidar biyayya ga shugaban ƙasa a zukatan duk wanda ke aiki tare da shi don samar da hadin kai, aiki tare don inganta Najeriya.

A dunƙule za mu iya cewa idan aka yi la`akari da irin matakan da gwamnatin shugaba Tinubu ta ɗauka, ko shakka babu Najeriya na gab da shiga ƙungiyar ƙasashen da suka ci gaba.

Nkwocha shi ne Babban Mataimaki na Musamman ga Shugaban ƙasa Kan Harkokin yaɗa Labarai Da Sadarwa a Ofishin Mataimakin Shugaban ƙasa

Leave a Reply