Illar amfani da lemon tsami ga ‘ya mace

Daga AISHA ASAS
A yau za mu taɓo ɗaya daga cikin matsalolin da rashin sani ko in ce yarda da duk wani abu da aka ce na qarin ni’ima ke janyo mana.

Idan mun ɗauki kafafen sada zumunta a misali, wuri ne da ya haɗa masu ilimi da kuma mashiririta da ke neman janyo hankalin mutane ta kowacce hanya, ko don samun mabiya da yawa ko kuma don a ce sun iya.
Wannnan kan sa su dinga ƙirƙirar ƙarya ko amfani da wani abun da ba su fahimta ba wurin yaɗa abinda zai iya cutar da mutane. Za ku iya yarda da zance na idan kun yi duba da cewa, har hadisai na ƙarya ake faɗa a kafafen sada zumunta. Idan kuwa mutum zai zauna ya tsara ƙarya ya danganta ta da manzon rahma, waye ba zai iya yi wa ba?
A ɓangaren qarin ni’ima wannan matsala ta fi komai samun matsugunni, saboda yadda aka san mata da son abin da zai qara ni’imarsu ido rufe. Hakan zai sa duk wanda ke yawan ɗora sababbin hanyoyin ƙarin ni’ima zai yi saurin samun mabiya.
Abin takaicin shi ne, yadda muke saurin aminta da duk wani abu da ake sanar da mu na ƙarin ni’ima ba tare da la’akari da ‘isnadin’ abin ba. Ba ma tambayar kanmu shin ina shi mai faɗa ya samo, kuma ababen da ya ce za a iya haɗawa ko akwai mai cutarwa a ciki. A taƙaice ba ma neman masana kan sanin illa da amfanin ababen da ake shelanta mana suna da amfani ga jiki.
Zan bada misali da lemon tsami don a iya fahimta ta. Sanannen abu ne an jima ana sanar da lemon tsami a matsayin wata hanya ta gyara mace, yana kawar da ciwon sanyi, yana warkar da matsalar warin gaba, sannan yana taimakawa wurin qara wa mace ɗanɗano. Da yawa a mata sun yi amfani da shi, kuma kaso mai yawa sun ga wannan ilimi ne a kafafen sada zumunta wadda ba su da tabbacin ma wanda ya yi rubutun, kuma a haka suka yarda da shi, suka yi amfani.
Tabbas lemon tsami na kawar da qwayoyin cuta sosai, ba akan mutum kawai ba har wasu ababe na amfani, kuma yana ɗaya daga cikin ababen da ƙarfin su kan iya hana abu lalacewa, wannan ke sa a sanya su a wasu ababen ci da sha kamar sovo don ya kawar da abinda zai sa wannan abinci ya yi saurin lalacewa.
Kunga kuwa zai iya yin tasiri wurin kawar da qwayoyin cuta da aka ɗauka a banɗaki ko waɗanda suka taru suka kawo warin gaba na daga rashin tsafta da sauran su. Sai dai inda gizo ke saƙa shi ne, rashin sani ya sa ba mu san cewa, farjin mace karan kansa yana samar da qwayoyin na cuta, kuma a cikin su da dama yana yin su ne don amfanin farjin, ba wai don ya kawo masa matsala ba. A taqaice farjin mace na amfani da wasu ɓangare na waɗannan ƙwayoyin cuta wurin zamansa a yanayin da ake buqatar shi, ciki kuwa har da ma yanayin sha’awar da mace ta ke da ko ta ke samu.
To, a lokacin da ki ka yi amfani da lemon tsami, ba shi da matata da zata bambance masa qwayoyin cutar da zai kashe da waɗanda zai bari a raye, don haka sai ya yi masu mai gabaɗaya. Hakan idan ya kasance yana faruwa na wani tsayin lokaci, zai iya taɓa ni’imar mace kuma zai yi tasiri wurin samar da ƙarancin ni’ima, wanda ga mai hankali zai fahimci illarshi ta fi amfanin shi yawa, don haka barin shi a nemi wani da bai tare da cutarwa ne zai fi.