Yadda za a samu maslaha tsakanin surukai (2)

Barkanmu da jimirin karatun jaridarku mai farin jini ta Manhaja. Za mu ci gaba daga inda muka tsaya a kan dalilan da suke kawo lalacewar alaƙa tsakanin surukai. Kamar yadda muka faɗa a makon da ya gabata, surukuta a ƙasar Hausa ta zama kamar gaba a tsakaninsu. Kowa kishi da hassada yake wa ɗanuwansa. Ga rainin wayo, abin ba a magana.
A makon da ya gabata mun fara kawo wasu daga cikin dalilan da suka sa hakan take faruwa domin masu karatu su yi alƙalanci su gano wai shin ma laifin wanene? To a yanzu za mu ci gaba da kwararo muku bayani a kan wasu dalilai da suke jawo hakan da ma neman mafita. A sha karatu lafiya.

Abu na gaba shi ne: Akwai kuma faɗar laifin juna wajen iyaye. Kamar yadda Bahaushe yakan ce zo mu zauna, zo mu saɓa. Haka ma ma’aurata rayuwarsu tamkar kurɓa ne daga kuttun zuma gauraye da maɗaci. Akan yi daɗin. Haka ma idan saɓanin ya zo akan saɓa. Wani zubin ma a yi kaca-kaca. Amma da yake mata da miji sai Allah, sai ka ga an dawo an ɗinke kamar ba a yi ba.
To inda matsalar take shi ne, idan aka sanar da iyaye wasu abubuwan da aka yi na ɓacin rai, su iyayen ba sa iya mantawa ko da kuwa su ma’auratan sun manta kuma sun yafe wa juna. Amma su iyayen matar kullum kallon surukin nasu suke yi da wancan halin. Haka shi ma mijin a nasa ɓangaren kullum iyayensa kallon matarsa suke da wannan halin. Ba za su iya yafe mata ba ko da shi ɗan nasu ya yafe mata sun shirya. Kuma daga haka alaƙar surukan idan ba wani ikon Allah ba, ta taɓarɓare kenan.
Sannan akwai ramuwa. Akwai wani lokaci da idan aka samu namiji mara kyautata wa surukansa. Wani lokacin ma har iyayen matar yakan kama ya zage su tas kai ka ce ya samu zogale. Irin haka idan ta ci gaba, ita ma matar takan fusata har ta kai bango ita ma ta daina kyautata wa iyayensa shi ma. Domin za ta ga ai iyaye ba su fi iyaye ba. Don haka ita ma sai ta shiga cin zarafin nasa iyayen.
Sai kuma rashin kyautatawa. Haƙiƙa kyautatawa tana ƙara ingancin kowacce irin alaƙa. Kamar yadda rashin kyautatawar kan rusa alaƙa. Dan Adam yana son mai kyautata masa kamar yadda ya zo a hadisin Annabi (SAW) cewa, Zuciya tana da halayya guda biyu; son mai kyautata mata, da ƙin mai munana mata. Rashin kyautata wa surukai da cutar da su walau iyayen mijin ko matar ɗa, yana sanya ƙiyayyar mai yi a zuciyar wanda ake cutarwar. Kuma dafin ƙiyayya yana da wahalar magani.
Sai kuma rashin kyautata wa iyaye da dangi. Yawanci a ƙasar Hausa in dai namiji yana da hali, za a ga yana yi wa iyaye da ‘yanuwa har ma da abokanen arziki hidima mai yawan gaske. To duk lokacin da aka samu akasin haka kuma, wato ba ya wa iyaye da dangi hidima. Ko kuma hidimar da yake musu ba ta kai yadda suke tsammani ko son ya dinga yi musu ba, sai a ɗauki gaba da matarsa. A ce ya tattare a gindinta. Musamman ma idan ana ganinta fes-fes kullum ita da ‘ya’yanta.
Ko da kuwa ita matar tana da wata sana’a da take yi dai ba za ta fita a wajen waɗancan surukai ba. Su kawai duk abinda ta yi ɗansu ne ya yi. Haka kurum sai a ɗauki karan tsana a ɗora wa baiwar Allah.
Zargi da rashin fahimtar juna: Wannan shi ma wata hanya ce da take kawo tangarɗa a alaƙa tsakanin mutane. Zargi mugun abu ne da musulunci ya yi hani da shi. Yanke wa wani hukunci a igiyar zato yana ɓata alaƙa sosai. Shi zargi shi ne mutum ya dinga tunani ko zaton abinda babu shi. Misali mutum ya yi abu kai kuma ka dinga tunanin wani abu daban da ba shi yake nufi ba. Kuma rashin fahimar halin juna shi yake kawo zargi. Idan surukai ba za su yi amfani da zahiri wajen mu’amalantar juna ba, sai dai a ɗora komai bisa zargi, to lallai za a samu matsalar rashin jituwa. Misali kamar mace da miji suna zaman lafiya cikin soyayya da lumana sai a dinga zargin cewa ta asirce mijin har ta mallake shi. Wanda wani lokacin ba gaskiya ba ne. Hakan zai sa surikai su ƙullace ta. Musamman ma idan bayan aurenta ɗansu ya daina yi musu hidima yadda ya saba. Ba za a duba hidimomi ne suka qaru a kansa ba. Yanzu yana riƙe da gidaje biyu ne a maimakon guda ɗaya kacal da yake riƙewa a da.
Ina fata dai masu karatu za su karanta a nutse su yi mana alƙalanci su ga wai shin wanne ɓangare ne yake da laifi? Iyayen miji ne, ko na mata, ko kuma matar ɗa ko mijin ‘yar? Kuma ina fata waɗanda suke da waɗannan halaye su yi ƙoƙari su gyara. Domin yau gare ka ne, gobe ga wani. Ma’ana idan ka yi amfani da wata dama ka cutar da wani, gobe kuma Allah zai iya ba wa wani dama kai ma ya cutar da kai. Sai mun haɗu a wani makon. Ina godiya matuka ga makarantana.

Leave a Reply