Sarakunan gargajiya da aka tsige a tarihin Nijeriya

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Mutane da dama suna tunanin cewa rikicin masarautar Kano ne karon farko da aka fara tsige sarkin gargajiya a tarihin Nijeriya, amma hakan ba gaskiya ba ne domin kuwa an sha tsige sarakuna a tarihi, wanda ya sa jaridar Blueprint Manhaja ta ga ya dace ya kawo tarihin tsige sarakuna a Nijeriya.

  1. Ooni na Ife – Ogboru: Ogboru shi ne aarni na 19 Ooni na Ife wanda sarakunan fadar Ife suka tsige daga gadon sarauta bisa zalunci wanda aka gaji da mulkinsa na shekaru 70. An yaudare shi da dabara ya fito daga wurinsa ya zo ya ga wani abu a dandalin Atiba na tsohuwar garin Ile-Ife kuma ba a bar shi ya sake komawa fada ba. A fusace ya nufi wata jirgi inda ya kafa wani karamin gari mai suna Ife-Odan ya zauna a can. Ooni na Ife kamar 6 da aka naɗa bayansa ya rasu ne a jere ba tare da wata 6 ba kamar wata siddabaru da aka yi a karagar mulki kuma sai da sarakunan Ife suka neme shi a Ife Odan domin ya dawo, amma ya bijirewa yunqurin ya ba su ’yarsa Moropo don yin wasu sadaukarwa a fadar ɗansa Giessi ya zama Ooni na gaba bayansa.
  2. Sarkin Bauchi – Umar Mohammed: An tuhumi Mohammed a ranar 16 ga Fabrairu, 1902 ta hannun Lord luggard na biyu a matsayin William Wallace saboda zargin mu’amalar bayi da rashin biyayya ga gwamnatin Biritaniya da kuma rashin mulkin mutanensa yadda ya dace. An naɗa ɗansa a matsayin sabon sarki.
  3. Sarkin Kano Aliyu Ibn Abdullahi Maje Karofi: Ya zama Sarkin Kano a shekarar 1894 bayan rasuwar Sarki Muhammad Bello, kuma yaƙin basasa na “Bassa” da ake kira yaƙin basasar Kano na uku ya fara shi, tare da babban yayansa Yusuf lokacin da Sarkin Musulmin Sokoto ya sanar da wani basarake da ake kira Tukur a matsayin sabon Sarkin Kano. Yaƙin dai ya ɗauki tsawon shekara guda ana kiran Aliyu da Sango na zaki (mai gudu) ko Ali Balads, saboda yawan amfani da bama-bamai a mafi yawan yaqe-yaqen da ya ci Kano ya zama sarki a 1894. An tuɓe shi a shekara ta 1903 bayan ziyarar mubayi’a ga Sarkin Musulmi a Sakkwato lokacin da sojojin Birtaniya da Faransa suka kai wa Kano hari suka kawo qarshen mulkinsa. Da farko ya yi gudun hijira zuwa Yola daga baya Lokoja, mazaɓar sabuwar gwamnatin Arewacin Nijeriya inda ya rasu a shekarar 1926.
  4. Sarkin Ningi – ɗan Yaya: An kori ɗan Yaya ne a hedikwatar sojojin Birtaniyya watanni bayan an sallami Umar Sarkin Bauchi a watan Yuli 1902, saboda ta’addanci ga mutanensa da suka kai ga kashe wani mallam, tare da goyon bayan Sarkin Bauchi. An naɗa sabon Sarkin Ningi wanda shi ne magaji, mai suna Mammadu. Ɗan Yaya ya tsere zuwa garin Bura inda daga qarshe ’yan qabilar Bura suka kashe shi saboda ta’addancin da ya ci gaba da yi a shekarar 1905.
  5. Olu na Warri – Erejuwa I: Erejuwa shi ne sarkin gargajiya na Itsekiri sau biyu mabanbanta tsakanin 1951-1964 da 1966–1989. Wani babban jami’i a UAC kafin ya zama sarki, abin takaici ne jam’iyyar NCNC ta gabas ta tsige shi a shekarar 1964, saboda goyon bayan da yake baiwa ƙungiyar Awolowo Actions, wadda ita ce jam’iyyar fitattun Itsekiri. Sakamakon hamayyar siyasa ya kai ga kafa Jihohin Tsakiyar Yamma a lokacin. An mayar da Erejuwa zuwa wani gari mai suna Ogbesse, bayan da gwamnatin mulkin soja ta David Ejoor ta mayar da shi a shekarar 1966 ya kuma yi mulki har zuwa 1989.
  6. Alaafin na Oyo – Oba Adediran Adeyemi II: Oba Adediran Adeyemi II mai shekaru 84 (mahaifin Alaafin na Oyo na yanzu, Oba Lamidi Adeyemi) an tsige shi ne saboda adawar siyasa da Cif Awolowo ya jagoranci gwamnatin yammacin Najeriya a lokacin da ya bada ra’ayinsa na siyasa da goyon bayan wata jam’iyyar adawa mai suna NCNC ƙarƙashin jagorancin Cif. Nnamdi Azikwe wanda rashin jituwa da rikici ya ta’azzara da shugaban ƙungiyar Awolowo Action na lokacin, Bode Thomas. An sallami Oba Adediran daga garin Oyo a watan Yulin 1955 kuma an yi masa hijira zuwa Legas inda Alhaji N.B Soule wani hamshaƙin attajiri ne na NCNC ya zauna da shi, daga nan kuma aka naɗa Gbadegesin Ladigbolu a matsayin sabon Alaafin Oyo har zuwa 1970.
  7. Timi bw Ede – Abibu Lagunju: Timi Abibu Languju ya kasance Sarkin Yarbawa Musulmi na farko a tarihi wanda ya yi sarauta tsakanin 1855 zuwa 1892 kuma gwamnatin Birtaniya ta kore shi tare da mayar da shi Ibadan inda ya zauna tare da Sunmonu Apampa, Asipan Ibadan a lokacin kuma ya rasu a shekara ta 1900. Ɗaya daga cikin ’ya’yansa Raji Lagunju, wanda matar Ile-Ife ta haifa, an mayar da shi garinsu, ya zama babban Limamin Ile-Ife na biyu.
  8. Awujale na Ijebu-Ode Oba Adenuga 1892 -1925: An mai da Awujale Adenuga Folagbade ɗan Awujale na Ijebu Ode a watan Nuwamba, 1925. Yana da shekaru 33 kuma yana zaune da mahaifiyarsa a Igbeba, wani ƙaramin ƙauye kusa da Ijebu Ode. Shi ne zavin “Odi”, (Ijebu kingmakers) na gidan sarautar Tunwase amma zavinsa bai yi wa wasu sarakunan yankin dadi ba waɗanda suke ganin bai kai ƙarami ba kuma bai kai ga gaci ba. Daga ƙarshe an kore shi a shekarar 1929 aka kai shi Ilorin, saboda almundahana a kan kuɗin gandun daji da kuma tasiri wajen zaɓen Oba Onipe na IBU. Oba Ogunnaike ya gaje shi wanda kuma ya rasu a shekarar 1933.
  9. Akarigbo na Remo – Oyebajo: Oba Oyebajo shi ne sarkin gargajiya na Ijebu remo, a tsakiyar shekarunsa ashirin, ya kuma yi sarauta tsakanin 1811 zuwa 1915. Turawan Ingila sun kore shi daga muqaminsa saboda kasancewarsa basarake wanda ya qi girmama manyan sarakunansa.
  10. Osemawe of Ondo – Oba Adekolurejo Jimosun II (Otutubiosun): Oba wanda mulkinsa ya kasance daga 1918 zuwa 1925 an cire shi aka kore shi zuwa Ile-Ife a 1925, inda ya rayu kuma ya rasu. A zamanin mulkin Oba Jimosun ne garin Ondo yake da makarantar sakandare ta farko, wacce ake kira ‘Ondo boys high school’.

Za mu cigaba a mako na gaba.