12
Jun
Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Babbar Kotun Jihar Filato mai lamba ta 17 ta yanke hukuncin cewa, duk wani Bahaushe da aka haifa kuma ya taso a ƙaramar Hukumar Jos ta Arewa yana da cikakken haƙƙin a ɗauke shi a matsayin ɗan asalin yankin. Alƙali C. Donglong ne ya yanke hukuncin yayin da yake yanke hukunci a ƙarar da Fatima Baba Akawu da Baba Alhaji Akawu suka shigar a gaban kotun kan ƙin ba Fatima takardar shaidar asali (Certificate of Indigene) daga ƙaramar Hukumar Jos ta Arewa. Masu ƙarar sun nemi kotun ta tantance ko Fatima Baba Akawu, wadda aka haifa…
