2027: Yadda hukuncin kotu zai rikita ADC da PDP

Spread the love

*Ana cikin zaman ɗar-ɗar bayan da Kotun ƙoli ta jinkirta yanke hukunta

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

A wani sabon salo na rikice-rikicen dambarwar siyasa da suke ƙara dagula harkokin jam’iyyun adawa a Nijeriya, Kotun ƙoli ta Nijeriya ta jingine yanke hukunci kan shari’un da suka shafi rikicin shugabanci a cikin jam’iyyun ADC da kuma PDP, lamarin da ya haifar da damuwa da zaman ɗar-ɗar kan yiwuwar shigar su babban zaɓen 2027.

Kwamitin alƙalai biyar ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Mohammed Lawal Garba ne ya sanar da cewa, za a fitar da ranar yanke hukunci bayan kammala gabatar da hujjoji daga ɓangarorin da ke ƙara da kuma waɗanda ake ƙara.

A ɓangaren ADC, shugaban jam’iyyar na ƙasa, David Mark, ya shigar da ƙara yana ƙalubalantar hukuncin Kotun ɗaukaka ƙara da ya yi watsi da ƙarar tasa bisa hujjar rashin inganci. Mark na neman Kotun ƙoli ta dakatar da aiwatar da wannan hukunci.

Tun da farko, kotun ɗaukaka ƙara a ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Uchechukwu Onyemenam ta amince da ƙin amincewa da ƙarar da tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar na ƙasa, Nafiu Bala Gombe, ya gabatar, tana mai cewa ƙarar Mark ta ƙunshi batutuwa da ba su cikin hukuncin kotun farko.

Rikicin ya samo asali ne daga hukuncin Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ƙarƙashin Mai Shari’a Emeka Nwite, wadda ta ƙi bayar da umarnin dakatarwa da aka nema a watan Satumba na 2025.

Wannan rikici ya sa Hukumar Zaɓe ta ƙasa (INEC) ta janye amincewa da ɓangarorin biyu na jam’iyyar ADC tun ranar 1 ga Afrilu, tana mai cewa za ta ci gaba da zama a tsaka-tsaki har sai an samu hukunci na ƙarshe daga kotu.

Babbar matsalar ita ce, hakan yana nufin akwai yiwuwar har a rufe karɓar sunayen ’yan takara, ADC ba ta samu damar miƙa nata ba kenan tunda INEC ta ƙi amincewa kowane ɓangaren shugabanci na jam’iyyar.

A gefe guda kuma, rikicin PDP ya shafi ɓangaren shugabanci da Kabiru Turaki ke jagoranta, wanda ke ƙalubalantar hukuncin kotuna da suka soke babban taron jam’iyyar da aka gudanar a Ibadan a watan Nuwamba na 2025. Hukuncin ya amfanar da wani ɓangare na jam’iyyar da ake dangantawa da Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike.

Masu ruwa da tsaki na ci gaba da nuna damuwa cewa, jinkirin hukuncin na iya shafar shirye-shiryen jam’iyyun biyu, musamman ganin cewa, INEC ta tsara jadawalin gudanar da zaɓen fidda gwani tsakanin 23 ga Afrilu zuwa 30 ga Mayu, 2026.

Ana ganin cewa, hukuncin Kotun ƙoli zai yi tasiri sosai, ba kawai ga makomar jam’iyyun ba, har ma da yanayin siyasar adawa gaba ɗaya gabanin babban zaɓen 2027. Masu nazari na da fargaba da hasashen yiwuwa shiga babban zaɓen 2027 ba tare da manyan jam’iyyun adawa a Nijeriya ba, saboda tarnaƙin shari’a kurum, amma ba na rashin ƙaƙƙarfar adawar ba.

By ukarofi