Babban Labari

Harin Boko Haram ya halaka janar a Borno

Harin Boko Haram ya halaka janar a Borno

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Wasu da ake zargin ’yan ta’addan Boko Haram/ISWAP ne sun kai wani mummunan hari da tsakar dare a garin Benisheikh da ke ƙaramar Hukumar Kaga a Jihar Borno, inda suka hallaka wani babban jami’in rundunar soji, Birgediya Janar O. O. Braimah. Rahotanni sun bayyana cewa marigayin ya kasance kwamandan rundunar haɗin gwiwa a yankin, kuma ya rasu ne yayin da yake jagorantar dakarunsa a fafatawar da suka yi da maharan. Majiyoyi daga yankin sun tabbatar da cewa harin ya faru ne da misalin ƙarfe 1 na dare ranar Alhamis, a wani salo na hare-hare da aka…
Read More
Yadda sabon rikicin Jos ya dawo ɗanye

Yadda sabon rikicin Jos ya dawo ɗanye

*IGP Disu ya ziyarci Filato  *'Yan majalisun tarayya daga Filato sun kai ziyarar jaje Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU, a Jos  Al'ummar garin Jos, Babban Birnin Jihar Filato, sun sake shiga wani sabon ruɗani da firgici sakamakon ɓarkewar wani sabon rikici, wanda ya samo asali daga harin ’yan bindiga da aka kai wani yanki na unguwar Rukuba da ake kira Gari Ya Waye, inda ake cin kasuwar dare da mashaya. An kai wannan hari ne ranar Lahadi, 29 ga Maris, 2026, da daddare da misalin ƙarfe 8:00 na dare, yayin da yankin ke tsaka da hada-hada, kamar yadda aka saba. Wannan…
Read More
A wane hali Sheikh Khalifa Zaria ke ciki?

A wane hali Sheikh Khalifa Zaria ke ciki?

*Jita-jitar rasuwarsa a hannun hukuma ta fara yawa *An kama shi bisa zargin hannu a juyin mulki Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Ana ci gaba da nuna damuwa a Nijeriya game da raɗe-raɗin rasuwar malamin addinin Musulunci a ƙasar, Sheikh Sani Abdulkadir Khalifa Zaria da ke tsare a hannun Hukumar Tsaron Farin Kaya ta (DSS). Tun bayan ɓullar wani bidiyo a shafukan sada zumunta da wani matashi ya yi iƙirarin rasuwar malamin, hankula suka tashi a sassan ƙasar musamman daga iyalai da ɗalibansa. Masu rajin kare haƙƙin ɗan'adam da manyan 'yansiyasa a ƙasar na ci gaba da yin tambayoyin…
Read More
Nijeriya ba ƙashin yarwa ba ce, inji Sarki Charles

Nijeriya ba ƙashin yarwa ba ce, inji Sarki Charles

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Ziyarar aiki ta tarihi da Shugaban Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya kai ƙasar Birtaniya ta kai ƙololuwa a ranar Laraba, yayin da shi da Sarkin Birtaniya, King Charles III, suka gabatar da muhimman jawabai a wata babbar liyafar gwamnati da aka shirya a Fadar Windsor da ke Ingila, inda sarkin ya bayyana Nijeriya a matsayin ƙasar da ba ƙashin yarwa ba. Rahotanni sun nuna cewa taron, wanda ya samu halartar manyan ‘yan gidan sarauta ciki har da Sarauniya Camilla da Yarima William tare da Catherine, Yariman Wales, ya sake jaddada dangantaka mai ƙarfi da tarihi tsakanin…
Read More
Kisan Ayatollah: Ba makawa sai mun ɗauki fansa – Iran

Kisan Ayatollah: Ba makawa sai mun ɗauki fansa – Iran

*An yi mana kisan ƙare dangi, inji Mojtaba Khamenei *Amurka ta kashe Dala biliyan 11 a kwana shida na yaƙin Iran Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Sabon jagoran addinin Iran, Mojtaba Khamenei, ya ce, Iran za ta ɗauki fansar mutanenta da aka kashe, ciki har da yara da ɗaliban makarantar Minab, baya ga jagoran addini, Ayatollah Khamenei da aka kashe a farkon yaƙinta da Amurka da kuma Isra’ila. Ya bayyana hakan ne a sanarwarsa ta farko da ya fitar tun bayan da aka naɗa shi a matsayin sabon jagoran addinin ƙasar wanda gidan talabijin gwamnatin ƙasar ta karanto. "Dole…
Read More
Yaƙin Iran ya zama barazana ga duniya

Yaƙin Iran ya zama barazana ga duniya

*Tattalin arziki da zaman lafiya na fuskantar rashin tabbas *Cikakken rahoto kan yaƙin da Amurka da Isra’ila ke yi da Iran Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Rikicin da ya ɓarke tsakanin ƙasashen Iran da Isra’ila tare da shigar ƙasar Amurka ya ƙara dagulewa bayan kashe jagoran addinin Iran Ayatollah Ali Khamenei a wasu hare-haren da Amurka da Isra'ila suka ƙaddamar. Bayan harin, Shugaban Amurka Donald Trump ya buƙaci al'ummar Iran su tuntsurar da gwamnatin ƙasar. Rikicin dai ya zama ɗaya daga cikin manyan batutuwan tsaro da siyasa da ke ɗaukar hankalin duniya a halin yanzu. Rahotanni daga manyan kafafen…
Read More
Yadda SSS ta saki Walida bayan shekara uku

Yadda SSS ta saki Walida bayan shekara uku

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Bayan kusan shekaru uku na ruɗani, zarge-zarge da muhawara mai zafi a faɗin ƙasa, Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (SSS) ta miƙa Walida Abdulhadi Ibrahim ga gwamnatin jihar Jigawa. A daren Laraba ne gwamnan jihar Jigawa, Umar Namadi, ya karɓi Walida a hedikwatar DSS da ke Abuja da misalin ƙarfe 10:40 na dare, bayan makonni na matsin lamba daga ƙungiyoyin farar hula da kuma sa ido daga jama’a. Da yake jawabi bayan karɓar, Gwamna Namadi ya bayyana Walida a matsayin “’yar jihar Jigawa,” yana mai ba da tabbacin cewa gwamnatin jihar za ta tabbatar da tsaron…
Read More
2026: Nasarori da akasin bikin kamun kifin Argungu

2026: Nasarori da akasin bikin kamun kifin Argungu

*Yadda bikin ya zama na musamman a Afrika *An rasa rayukan mutum biyu *An sace fitilun da aka saka jim kaɗan bayan kammala bikin *An yi ƙorafi kan tsafta da kwamitoci Daga JAMIL GULMA a Birnin Kebbi Biki nan mai cike da tarihi da ƙayatarwa a Afrika na kamun kifi a Argungu, wanda ake gudanarwa shekara-shekara, yana ɗaya daga cikin bukukuwan nuna al'adun gargajiya da ake yi a garin Argungu da yake a Jihar Kebbi, inda nan ne cibiyar Daular Muhammadu Kanta, wanda yana ɗaya daga cikin gwamnonin Muhamma Askia na Masarautar Songhai a baya. Bikin kamun kifi na Argungu…
Read More
El-Rufai ya ƙi yarda a kama shi

El-Rufai ya ƙi yarda a kama shi

...Bayan isowarsa Nijeriya daga Masar Daga NASIR S. GWANGWAZO a Abuja Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya ƙi yarda da yunƙurin jami’an tsaron Nijeriya na su kama shi a filin jirgin saman Nnamdi Azikwe da yake a Abuja a jiya Alhamis. Blueprint Manhaja ta ruwaito cewa, a wani faifen bidiyo da aka wallafa a yanar gizo jiya, an ga El-Rufai yana magana da jami’an, waɗanda suka tunkare shi bayan ya sauka daga jirgi a yayin da ya ke dawowa daga Kairo, babban birni ƙasar Masar, amma sai tsohon gwamnan ya kafe kai da fata cewa, ba zai bi…
Read More
Sabuwar dokar zaɓe: Muhimman abubuwan da Majalisar Dattawa ta amincewa

Sabuwar dokar zaɓe: Muhimman abubuwan da Majalisar Dattawa ta amincewa

*Majalisar Wakilai ta kafa kwamitin daidaito Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Majalisar Dattawa ta Nijeriya ta zartar da dokar zaɓe ta 2022 da aka yi wa garambawul. An zartar da ƙudurin dokar ne bayan nazari da amincewa da sassa 155 da ke ƙunshe a cikin ta. ɗaya daga cikin gyare-gyaren da aka yi wa dokar ta 2022 shi ne rage wa’adin da Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta ƙasa (INEC) ke da shi na futar da sanarwar zaɓe daga 360 zuwa kwana 180. Hakan ya biyo bayan amincewa da ƙudirin da Sanata Tahir Monguno ya gabatar na rage kwanakin…
Read More