An sace fasinjoji a hanyar Ƙanƙara dake Katsina 

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Wasu ’yan bindiga sun yi sace fasinjoji da dama a wani harin da suka kai a Ƙaramar Hukumar Ƙanƙara da ke Jihar Katsina.

Lamarin ya faru ne a jiya Alhamis bayan da ’yan bindigar dajin suka tare wata mota ƙirar bas mai cin mutane 18 mai lamba 14B-300-KT cike maƙil da fasinjoji mallakar hukumar kula da sufuri ta Jihar Katsina (KSTA).

Wani ganau ya shaida wa majiyarmu ta wayar tarho cewa, galibin fasinjojin da ke cikin motar sun fito ne daga Ƙaramar Hukumar Funtuwa a kan hanyarsu ta zuwa Katsina, Babban Birnin Jihar Katsina.

Duk da cewa, hukumomin da abin ya shafa ba su ce uffan kan lamarin ba, amma shaidar gani da ido ya ce, lamarin ya faru ne a tsakanin yankin Burdugau da ’Yargoje kafin a isa garin Ƙanƙara da tsakar rana.

Yankin Ƙaramar Hukumar Ƙanƙara na ɗaya daga cikin ƙananan hukumomin jihar da ke kan gaba a Katsina ta Kudu wajen fama da matsalolin tsaro, inda ba mazauna yankin kaɗai ba, har da matafiya ke rayuwa cikin fargabar hare-haren ’yan bindigar daji a jihar ta Katsina.

Idan za a iya tunawa, matsalar tsaro ce ta tilasta wa sabuwar Gwamnatin Jihar Katsina a ƙarƙashin jagorancin Gwamna Dikko Umar Radda ta kafa rundunar yaƙi da ’yan ta’adda ta jihar, wacce ya rantsar da ita a kwanakin baya.

Bugu da ƙari, kusan dukkan jihohin yankin Arewa a Nijeriya bakiɗaya su na fama da matsalolin tsaro da suka haɗa da yin garkuwa da mutane tare da karɓar fansa, kisan kiyashi da makamantansu, inda aka shafe shekaru da dama a cikin wannan yanayi, lamarin da ya sanya a kullum Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ke cigaba da cin alwashin kawo qarshen matsalar, amma dai har yanzu yawancin al’ummar yankin ke kallon alƙawarin a matsayin gafara sa ba tare da an ga ƙaho ba.