Tare da BASHIR MUDI YAKASAI
Masana tarihi sun tabbatar da dalilai uku waɗanda sune tushen hulɗa a tsakanin nahiyoyin duniya. Dalilin farko shine ƙaurace-ƙauren mafarauta dana makiyaya da kuma masunta.
Na biyu tafiye-tafiyen fatake na ruwa dana hamadar sahara da kuma dazuka. Na uku shine gudun hijira don gujewa wasu masifu kamar girgizar ƙasa ko aman duwatsu na wuta ko ambaliyar ruwa ko gobarar daji ko kuma yaƙi da kuma yunwa a dalilin fari.
Amma dalilin zuwan Turawan yamma, wato ƙasashen Birtaniya da Faransa da Italiya da Potugal da Sapaniya da Jamus wannan nahiya ta Afrika shine fashi na al’ummarta da sunan cinikin bayi inda suka kwashi miliyoyin iyah Afrika ta yamma da Afrika ta Kudu zuwa Amurka ta Arewa (USA da Canada) da Latin Amurka wanda ya ƙasashe da suka haxa da Meziko, Bahamas, Dominikan Rifabulik, Guwatamela, Cuba, Hondurasa, Nakaraguwa, Hatti, Panama, Kolumbiya, Benezuwela, Guyana da Barazil dadai sauransu ƙasashe da suke wannan yanki domin yin bauta a gonaki da kuma guraren haƙar ma’adanai.
Bayan sun kwashe kusan shekaru ɗari suna kwasar bil adama daga wannan yanki sai suka sake dabara ta bautar da al’ummar Afrika a gidajensu da kuma sunan mulkin mallaka inda suka raba Afrika a tsakanin suka raɗa mana sababbin suna, inda mu suka sanya mana suna Nijeriya tun a shekara ta 1914. Tun wannan lokaci suke kwasar dukiyar ƙasar nan tun daga amfanin gona (auduga gyaxa kwakwar manja da koko da itacen timba) da ma’adunai irin su tama da bakin qƙarfe da kuza da tagulla da zinare da azurfa da daidai sauran ƙarafa masu daraja.
Bayan sun kwashi amfanin gona da ma’adanai wanda babu wanda zai ƙiddiga ton nawa suka kwasa har lokacin da suka yi mana ɗaurin talala da dabaibayi bayan sun turke mu a guri guda sanya da takunkumi da sunan samun ’yanci. Suka hana mu ilimi na kimiya da fasaha da kuma zamantakewa, suka bar mu da cin hanci da rashawa da ruf-da-ciki da dukiyar qasa. Suka koya mana sata da baba-kere da kwasar dukiyar ƙasa zuwa ƙasashen su da sunan “investment” zuba jari, wajen samar da aikin yi ga ’ya’yansu da jikikonsu mu kuma ko oho!
Su ne su ke kawo mana ƙwayoyi masu sanya maye domin haukata matasanmu maza da mata da qananan yara. Tun 1953 suke kwasar makamashin man fetur da gas da kuma dangoginsu.
Su suke hana matatun man fetur dinmu na Fatakwal da Warri da Kaduna su yi aiki domin ya zama wajibi mu saya a gurarensu. Kuma idan an tashi rabawa a kasa su za su yi farashi yadda za a siyar domin ba su wani kaso da sunan tallafi da kuma tallafi za su je biranen duniya su sayi filaye da giggina guraren shaƙatawa muna zuwa muna kallo da sunan yawan bude ido (tourism).
Wannan batu ba yau muka fara tattaunawa a wannan fili ba, mun tattauna fiye da takun masaki mun yi haka ne domin a fahimce mu cewa matsalar Nijeriya ba matsala bace da za mu ce matsala ce ta Allah da Annabi, wato “natural disaster” (bala’i daga indallahi) kamar yadda muka ambata a sama, dalilan da suke sa ɗan adam yin ƙaura daga wannan guri zuwa wani guri, ko kuma daga wannan nahiya zuwa waccen.
Matsalar Nijeriya, matsala ce shiryayya, wasu ne suka shirya suka tsara kuma suke tabbatar da an bi tsari daki-daki domin amfanin su, su da ‘ya’yansu su da jikokinsu har zuwa tattaɓa kunnensu har lokacin da duniya za ta tashi.
Tun daga matsalar bauta (slavery), zuwa mulkin mallaka da aikin tilas na giggina hanyoyin motoci da jiragen kasa da kuma tashohsin jiragen ruwa da biyan haraji launi-launi da haqar ma’adanai zuwa kasashen su da tilasa mana karatun book domin yi musu ayyukan da suke buƙata, wanda shi muke bi tun lokacin da suka ce sun bamu ‘yanci a shekara ta 1960, bayan sun fara kwasar man fetur da gas suna ba mu ladan gaba. Gashi yanzu sun saye ƙwaƙwalenmu, sun hanamu yin tunani irin namu sai tunani na wanda suka shirya.
An raba ma’aikaci da gaskiya da amana da aiki tukuru ya koma ha’inci, ƙarya da yaudara da kuma babakere da ruf da ciki da dukiyar kasa. Kowa daga shi sai ‘ya’yansa sai kuma abokan siyasarsa.
Saboda kada ayi maganin matsalolin sai aka ƙirƙiri talauci da fatara da yunwa da kuma rashin aikin yi. A ka fito da dabaru kullum talauci yana ƙaruwa ga jama’ar ƙasa, dukiyar ƙasa tana tafiya London da Paris da Lisbon da Berlin da kuma biranai da USA, kamar Boston da New York da San Francisco da Los Angeles da Las Vegas da kuma ƙasashen larabawa masu arzikin man fetur da gas.
Yaki da talauci da fatara da yunwa da kuma rashin aikin yi ga matasa maza da mata shine dawo daga rakiyar talaka domin kuwa an raba talaka da aiki ya koma cima zaune, baya son ya motsa sai a kawo masa dukkan abubuwan buƙata daga China ko Korea ta Kudu ko Taiwan ko Hong Kong ko Japan hatta shinkafa da alkama bukar talaka a kawo masa daga Thailand da Malaysia da Singapore da kuma Indonesia ko kuma a baban hawanmu na Adaidaita sahu daga India duk da cewa muna da Ajakuta da kuma guraren mulmula ƙarfe a Katsina da Sokoto da kuma Kano.
Lalaci shi yake kawo talauci da fatara da kuma yunwa, musamman ga ‘yan gata, mutanan da basa son su motsa.
Motis yafi labewa, inji Malam Aminu Kano. Haka Muhammadu Buhari ya tabbatar mana cewa ‘yan Nijeriya mutane ne “Cima Zaune” wannan Magana ta janwo masa bakin jinni.
Burin dan Nijeriya a buxe iyaka kasuwar yammacin turai da Asia su rika kawo mana kayayyakin da masana’antun su suka sarrafa, wato dai mu zama “Consumer Nation” wato, dabobbi masu ci da tuka kamar shanu da raƙuma da tumaki da kuma awaki.
Babban kuskuren da wannan gwamnati ta Bola Ahmad Tinubu da Kashim Shatima Mustpaha tayi ko kuma zatayi shine buɗe iyakokinmu da tsandauri da jamhuriyar Nijar da Benin da kuma Chadi da Kamaru.
Alfanan bude iyakokin tsandauri da ake tallatawa tsari ne na habaka gwanjan motoci da suture da kayayyakin lantarki, misali na’urorin sanyaya daki da ruwan sha. ‘Ya sumoga wato ‘yan fasa kwari sun sami dama su kasara sha’anin noma da kiwon tsintsaye, wato kaji da ƙwai su hana na cikin gida yin tasiri
Bari na sake baiyanawa, a dawo da rakiyar talaka, talakan Nijeriya shine dan maula da tumasanci da malaman tsibbu da bokaye da matsafa da yan bori abin bag a musulmi ba, ba ga kiristoci ba ga masu addinin gargajiya ba.
Abin kunya NIjeriya dake da jami’o’I da makarantun fasaha da kuma makarantun koyar aikin malanta da suke yaye dalibai sama da dubu hamsin shekara, amma dukkan su basa iya samar da abu guda ɗaya tak da sunan bincike da suka gudanar ya haifar da wannan nasarar.
Wani abu da yake daƙile qasar nan shine biyewa talaka daga koke-koken sa da kuma rashin dorewar shirye-shirye da tsohuwar gwamnati ta faro rimi-rimi, wato duk gwamnatin da tazo bazata dasa aiki akan inda ta bayanta ta tsaya ba, saboda kawai kukan talaka, sai ta wargaza ayyukan wadda ta shuɗe, kamar rufe iyakar tsandauri da Baba Buhari yayi.
Amma da anyi amfani da tsarin da tsohon gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya ɗora daga ayyukan da tsofaffin gwamnonin suka fara amma basu sami damar kammalawa har lokaci ya cimmasu.
Malam Ibrahim Shekarau da asibitocinsa har guda biyu da injiniya Rabiu Musa Kwankwaso da gadar sa ta sabon gari duk da cewa sun sami sabani na siyasa wannan abin yabo ne. kashi chasa’in (90%) cikin dari na koke-koken talakan Nijeriya, kuka ne na ‘yan gata saboda ƙoshi sai su ce da “Allah ya kashe su” kamar yadda na ga wata budurwa na faɗa kan an kawo mata abinci da naman kaza da ba a bare bayan kazar ba da aka soya, ita ba ta cin naman kazar da ba bare bayan ta ba. Don haka a dawo daga rakiya talaka.
