
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Hukumar Hana yi wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Ta’annati EFCC, ta kare matakinta na rufe asusun gwamnatin Jihar Osun, inda ta ce ta yi haka ne domin hana zargin karkatar da akalar dukiyar al’umma da ake bincike a kai kuma hakan ba shi da alaƙa da zaɓe mai zuwa.
A wata sanarwa da Jami’in Hulɗa da Jama’ar EFCC, Dele Oyewale ya fitar, hukumar ta ce yana da muhimmanci a kula da koken al’umma kuma a madadin a siyasantar da zarge-zargen yunƙurin.
A cewarta, ta fara bincike akan gwamnatin Osun ne tun a watan Maris, 2026 bisa zargin sauya akalar kusan Naira biliyan 11 da aka ware daga Asusun Kasafin Kuɗi na Tarayya (FAAC) zuwa asusun tallafa wa wasu al’amuran al’umma.
EFCC ta bayyana cewa, da dama daga cikin jami’an gwamnatin jihar ciki har da akanta janar ɗinta sun je gaban kwamitin bincikenta kan zargin badaƙalar bayan ya gayyace su.
Ta ce, duk da cewa an ɗauki tsawon watanni ana bincike, kaɗai abin da ta yi shi ne sanya asusun a tsarin “Post-No-Debit”, wato bin salon yadda ba za a iya cire wani kuɗi daga asusu sakamakon zargin wasu hada-hada aciki tun daga ranar 2 ga Agusta.
Ta ƙara da cewa, matakin nata ya yi daidai da ikon da doka ta ba ta na bai wa dukiyar al’umma kariya da kuma dakatar da laifukan da suka shafi kuɗi.

