Komai na mace yana da iyaka – Na’ima Daƙayyawa

Spread the love

“Babu wani abu da nake yi da nake so da ya wuce karatu da rubutu”

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU 

Marubuciya Na’ima Sulaiman Daƙayyawa ba ɓoyayyiya ba ce tsakanin matasan marubutan Hausa a Jihar Jigawa. Ta fito ne daga ƙaramar Hukumar Kaugama. Tana da gogewa a harshen Larabci da Hausa, inda yanzu haka take karatun digirinta na biyu a Jami’ar Sule Lamiɗo dake Kafin Hausa. Marubuciya ce da ta bambanta da sauran marubutan adabi, saboda ita ta fi mayar da hankali ne kan muhimman abubuwa na tarihi ko al’adu. Akasari rubuce-rubucen da ta yi sun shafi zamantankewar al’umma ne da tarihinsu. Littafin ta na farko, ‘Daƙayyawa Tsakiyar Kano’ ya samu karɓuwa sosai a wajen jama’a kuma ya buɗe mata ƙofar samun ɗaukaka da albarka a rayuwarta. A zantawarta da Abba Abubakar Yakubu ta shaida masa babban burinta na rayuwa. A yi karatu lafiya. 

MANHAJA: Mu fara da jin cikakken sunanki da abubuwan da ki ke yi a rayuwar ki ta yau da kullum.

NA’IMA: Sunana Na’ima Sulaiman Daƙayyawa. Ni marubuciya ce, ɗaliba, malama, ýar kasuwa, kuma uwa.

Ko za ki gaya mana tarihin rayuwarki? 

Ni haifaffiyar garin Daƙayyawa ce, a ƙaramar Hukumar Kaugama da ke Jihar Jigawa.

Kasancewar mahaifina ma’aikacin gwamnati ne mun yi zama a garuruwa daban-daban a  nan Jihar Jigawa, waɗanda suka haɗa da Babura, Kazaure, Kafin Hausa da Birnin Kudu. Wannan ce ta sa gaba ɗaya rayuwarmu mun yi ta ne tamkar mutanan nan da ake kira Bararoji, wanda suke yawo daga wannan gari zuwa wancan. 

Bisa ga haka ne ma na yi  karatuna na firamare da sakandire duk a garin Baɓura, inda na halarci makarantar sakandiren ýammata ta kwana da ake kira da Goɓernment Girls Arabic Secondary School Baɓura. A ɓangaren karatun addini kuwa na yi saukar Alƙur’ani da hadda a makarantar Tahfizul ƙur’an. Na kuma yi Diploma a Kwalejin Nazarin Ilimin Shari’a da Sauran Darussa ta Yusuf Bala Usman da ke garin Daura a Jihar Katsina, inda na karanci fannin nazarin harshen Larabci da Hausa.

To, bayan nan ne kuma sai na tsunduma cikin kogin soyyaya. Allah kuma Ya ƙaddara min yin aure wanda shi ne dalilin da ya kawo min tsaikon cigaba da karatuna, duk da auren da na yi bai zama silar rushewar cigaba da karatun nawa bakiɗaya ba. Sai dai na samu jinkiri wanda har sai da na haifi yara guda biyu, kafin mahaifina ya ga dacewar na cigaba, mijina kuma ya aminta da hakan a wancan lokacin na koma yin digiri ɗina na farko. A Jami’ar Sule Lamiɗo dake Kafin Hausa a nan Jihar Jigawa na karanci ilimin harshen Larabci, wato B.A Arabic.

Ina cikin karatun ne kafin na kammala na haifi yarinyata ta uku. A yanzu haka dai na ɗora ina cigaba da karatuna na digiri na biyu, duk dai a nan Jami’ar Sule Lamiɗo dake Kafin Hausa.

Wanne abu ne ya kasance tsani a rayuwarki, wanda yake baki ƙwarin gwiwa tun tasowarki har zuwa yanzu?

Maihaifina shi ne ya kasance silar samun duk wata nasara a rayuwata. Shi ne wanda ya zama bango a gare ni, a duk lokacin da wata gazawa ta zo min, ko wani rauni dake ƙoƙarin kai ni ƙasa. Shi ne wanda nake dafawa, kuma yake riƙo ni da dukkan hannayensa, kai har da gangar jikinsa bakiɗaya, har ya kai ni ga matakin nasara.

Sannan kuma mahaifiyata ce ta zame min allon kwaikwayona, don da tarbiyyarta ne na rayu, kuma duk wani ƙalubale da ya tunkaro ni, ita ce wacce take yin uwa ta yi kaka wajen ganin komai ya daidaitu.

Allah dai Ya sakawa iyayenmu da alkairi, ya sa su yi kyakyawan ƙarshe.

Kasancewarki ‘ya mace wacce gwagwarmaya ki ka fuskanta wacce ki ke ganin da a ce ke namiji ce da ba haka abin zai zama ba?

A wannan ƙadami ne ya kasance ba mai sauƙi ba, musamman ta yadda al’ummarmu suke. A yau idan har ‘ya mace ta bigi ƙirji ta ce ita fa so take yi ta zama ‘yar gwagwarmaya, ma’ana tana son ba da wata gudummawa ga al’ummarta to, daga nan ne za a fara mata wani irin kallo na daban, musaman idan ya zamana ba ta da aure, Budurwa ce ko kuma Bazawara, wannan lamari yana ci min tuwo a ƙwarya.

Wataƙila da ni Namiji ce, ba haka abubuwan za su kasance ba, zan iya cimma wasu burika da suke nuƙurƙusata a zuci, zan tashi, zan faɗi, domin dai kawai na ga na tsira da mutuncina da kuma kawo sauyi a rayuwar al’umma bakiɗaya. Sai dai kash, na zo a mace! Ita kuwa ýa mace komai nata yana da iyaka, da zarar kuwa ta ce za ta ƙetara iyakarta to, daga nan ne fa ta saya wa kanta zato, kawo farmaki kala-kala, wanda ba ta san ina ne makomar rayuwarta daga ƙarshe ba.

Mene ne alaƙarki da rubuce-rubuce da karatu, kina samun damar yin karance-karance?

Alaƙata da rubuce-rubuce tamkar dai hanta da jini ne, wanda ake cewa ba sa rabuwa, domin kuwa ni rubutu abu ne da yake ƙara faɗaɗa min tunani, kasancewata ɗalibar harshe, kuma abu ne da ya kasance mafi soyuwa a gareni. Duk lokacin da ya zamana mutum yana da sha’awar yin bincike to, ba a raba shi da karance-karance. A halin yanzu babu wani abu da nake yi wanda nake so a karan kaina wanda ya wuce karatu da kuma rubutun, su kuwa sun haɗa da irin rubuce-rubucen marubuta, don ƙara samun buɗar ido da ganin fikirorin magabata, da kuma kyautata nawa rubuce-rubucen, da ma neman ilimin baki ɗaya.

Wanne littafi ki ka taɓa karantawa wanda ya tsaya miki a rai, kuma har yanzu kin kasa mantawa da shi? Me ya sa ya yi tasiri a wajenki?

Kasancewar mahaifiyata mace ce mai zafi sosai akan sha’anin tarbiyya, sam ba ta  barina na yi karatun littafi na nishaɗi ko na zamantakewa. Sai dai akwai wani littafi da na karanta mai suna, ‘Namiji Ba Ya Kaɗan,’ duk da dai ba zan iya tuna sunan marubuciyar littafin ba, amma tabbas littafin ya tsaya min a rai kuma na jinjinawa marubuciyar sosai. Dalili kuwa shi ne darussan da ke cikin labarin suna da yawa. Sannan kuma na karanta wani littafi mai suna, ‘Yartsana na Dakta Ibrahim Sheme, a wannan littafin na ƙara tabbatarwa lallai marubuta ‘yan baiwa ne.

Kawo yanzu kina ganin kin karanta littattafai sun kai nawa?

Kamar yadda na faɗa a baya, ban tsunduma cikin karatun littatafai ka’in da na’in da wuri ba, har sai da na shiga cikin harkar rubutu. Sai dai duk da haka na karanta littatafan da ɗan dama, da ba zan iya faɗar adadin su ba. Kuma a dalilin karance-karancen da na yi ne na haɗu da abubuwan mamaki daban-daban, wanda a gaskiya ina jinjina wa tsofaffin hannu, wato iyayenmu a fagen rubutu.

Har yanzu kina samun lokacin yin karatu? Wanne littafi ki ke karantawa a yanzu?

Kasancewar kamar yadda na gaya ma a baya, ina kan cigaba da karatun digirina na biyu, ba na samun isasshen lokacin karatun wasu littattafai na daban da ba su shafi karatun da nake yi ba. Sai dai jifa-jifa ina ɗan duba wasu littattafai na onlayin,  kamar a yanzu haka akwai littafin da nake karantawa mai suna ‘Sartse’ na Sani Muhammad Lawan, wanda ake kira Sayyid. 

Akwai kuma gajerun labarai da nake karantawa waɗanda ba su da yawa sosai, saboda rashin samun lokaci. 

Ina jin daɗin karanta littattafan marubutan adabi na Hausa sosai, waɗanda idan na samu zarafi nake dubawa, kamar irin littattafan da su Nasiru Kainuwa, Ayuba Muhammad ɗanzaki, Jibrin Yusuf Kaila, da su Hajara Ahmad Maidoya ke rubutawa, saboda ina ƙaruwa sosai da abubuwan da suke wallafawa da suka shafi ƙalubalen rayuwa daban-daban, mafita, nasara ko faɗuwa.

Daga wanne lokaci ki ka fara tunanin rubuta littafi na kanki?

Ba a jima sosai ba, a shekarar 2021 ne. Kuma na fara rubutu ne da littafin ‘Daƙayyawa Tsakiyar Kano’. 

Kawo yanzu kin rubuta littattafai sun kai nawa?

Kawo yanzu na rubuta littattafai sun kai  guda goma, wasu na kammala har sun fita ga jama’a wasu uma ina kan aik a kansu. Sun haɗa da littafin, ‘Daƙayyawa Tsakiyar Kano’, ‘Rana ɗaya’, ‘Yaye’, ‘Sankarar Mama’, ‘Kuɗin Ritaya’, ‘Karin Harshe A Masarautun Jigawa’, ’Yalleman Garin Waliyan Allah’, ‘ƙwalamammiya’, ‘Bara Akufai’, ‘Barin Halak Don Kunya’, da kuma ‘Farautar Mutunci’. Sai dai kuma akwai gajerun labarai da na yi da dama. Ina ɗauko abubuwan da suka shafi zamantankewa, musaman game da wata matsala da take faruwa, ko take damun al’ummarmu sai dai kuma a wasu lokutan ba a fiya ɗaukarsu a matsayin matsala ba. 

Daga ciki akwai labarin da na rubuta mai suna ‘Yaye’, wanda labari ne da ke nuna yadda iyaye mata suke yaye yara ƙanana, kuma suke amfani da maganin barci wajen hana yaro kukan dare, don gudun kar ya tashi yana neman mama. Akwai wasu iyayen da ke bai wa jariransu maganin sa barci wanda zai bugar wa da yaro ya yi ta barci, ba tare da ya fitini uwar da kuka cikin dare ba. Ka ga a nan uwa da kanta ta koya wa ɗanta shan kayan maye tun yana ƙadamin da bai san kansa ba. Hakan illa ce babba, sai dai ba kowacce uwa ce za ta fahimta ba.

Akwai kuma littafin ‘Farautar Mutunci’, wanda labari ne da ya shafi yadda al’umma ke kallon ‘ya mace bazawara. Daga lokacin da wata ƙaddara ta sa mace ta fito daga gidan mijinta to, daga nan ne wasu maza a gefe, ‘ya’yan Allah bani, za su fara kai miki farmaki, ko da kuwa baki da ra’ayin aikata abin da ba daidai ba. Amma ta ƙarfi da yaji sai sun yi ta ƙoƙarin ɓata miki syna da mutuncinki ko ta halin ƙaƙa, wanda ni ɗin nan ganau ce ba jiyau ba, sai dai in Allah ne Ya taimake ki ki ka sha da ƙyar.

Sannan shi littafin ‘Sankarar Mama’ yana magana ne kan yadda ciwon ya ke yin illa mai girman gaske a jikin ýa mace da yadda mutanan mu na karkara ba su farga da illolin ciwon ba, har ta kai ga dubban mata suna rasa ransu a dalilin sankarar mama.

Kin taɓa wallafa wani daga cikin littattafan da ki ka rubuta?

Za mu kwana a wannan tambayar, inda a mako na gaba za mu kawo maku amsar ta tare da wasu ƙarin tambayoyin. Duk dai tare da fasihiyar marubuciya Na’ima Sulaiman Daƙayyawa. Da yardar Mai Duka.

By ukarofi

Leave a Reply