Sojoji sun ga bayan Dogo Gide

Daga BASHIR ISAH

Rahotanni sun ce dakarun ƙasar Nijar sun ga bayan gawurtaccen ɗan bindigar nan, Dogo Gide, na mayaƙan ANSARU da sauran ƙungiyoyin ‘yan ta’adda.

MANHAJA ta kalato cewar, Dogo Gide ya mutu ne sakamakon raunin da ya ji biyo bayan musayar wutar da aka yi tsakanin rundunar haɗin gwiwa ta Operation Hadarin Daji (OPHD) a dajin Madada da yankin Ƙaramar Hukumar Maru a ranar 12 ga Maris, 2024.

An ce duk da raunin da aka yi injuries, Dogo Gide, sai da aka san yadda aka yi aka saci jiki aka shigar da shi asibiti a yankin Mabera a Sakkwato inda a nan ne aka ce rai ya yi halinsa.

Tsohon hadimin Shugaban Ƙasa, Bashir Ahmad, shi ne ya bayyana haka ranar Laraba a shafinsa na X.

“Na tashi da labari mai daɗi, cewar an ga bayan Dogo Gide. Gawurtaccen ɗan bindigar ya mutu ne sakamakon raunin harbin bindiga yayin musayar wuta da dakarun Operation Hadarin Daji (OPHD),” in ji Bashir.

Bayanai sun ce an saci jiki wajen shigar da Dogo Gide asibitin ne da taimakon wani jami’in tsaro wanda yake tsare a halin yanzu.

Wannan al’amari ya haifar da zargin cewar ko da haɗin bakin wasu manyan jami’an tsaro wajen hana ruwan yaƙi da matsalolin tsaro gudu a ƙasar.

Mutuwar Dogo Gide alama ce ta babbar nasara ga Sojojin Nijeriya, musamman ma rundunar haɗin gwiwa tsakanin runduna ta 1 ta sojin Nijeriya da runduna ta 8 ta sojin Nijar.