Lawal ya nemi taimakon Tinubu kan yaƙi da matsalar tsaro a Zamfara

Daga BASHIR ISAH

Gwamna Dauda Lawal na Jihar Zamfara, ya gana da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu inda suka tattauna batun tsaron Jihar Zamfara.

A ranar Talata suka yi ganawar a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja kuma cikin sirri.

Mai magana da yawun Lawal, Sulaiman Bala Idris, ya bayyana cewa Lawal ya yi wa Shugaba Tinubu bayani game da halin tsaron jihar Zamfara ke ciki, musamman sake dawowar hare-haren ta’addanci a jihar.

Idris ya ce shugannin biyu sun yi tattaunawa mai zurfi kan tsare-tsare da matakan da suka dace a ɗauka domin tunkarar matsalar tsaron da ta addabi Zamfara.

Daga cikin matakan da ganawar tasu ta nuna buƙatar a ɗauka har da yaƙi da talauci da rashin aiki wanda ake ganin su ne tushen matsalar rashin tsaro da sauran manyan laifuka a jihar.

Sanarwar da Idris ya fitar ta ce, “Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bai wa Lawal tabbacin mara masa baya ta hanyar samar masa da abubuwan da ake da buƙata wajen maido da tsaro da zaman lafiya a Zamfara.

“Yayin tattaunawar, Gwamna Lawal ya shaida wa Shugaban Ƙasa cewar, sama da shekara 13 Juhar Zamfara ta zama tamkar tungar ɓarayin daji a shiyyar Arewa maso-yammacin Nijeriya.

“Gwamna ya roƙi Shugaba Tinubu da ya tallafa masa ta hanyar tura ƙarin Sojoji da makamai kasancewar akwai ƙarancin sojoji da makamai a jihar,” in ji sanarwar.