Babban Labari

Sojoji sun ga bayan Dogo Gide

Sojoji sun ga bayan Dogo Gide

Daga BASHIR ISAH Rahotanni sun ce dakarun ƙasar Nijar sun ga bayan gawurtaccen ɗan bindigar nan, Dogo Gide, na mayaƙan ANSARU da sauran ƙungiyoyin 'yan ta'adda. MANHAJA ta kalato cewar, Dogo Gide ya mutu ne sakamakon raunin da ya ji biyo bayan musayar wutar da aka yi tsakanin rundunar haɗin gwiwa ta Operation Hadarin Daji (OPHD) a dajin Madada da yankin Ƙaramar Hukumar Maru a ranar 12 ga Maris, 2024. An ce duk da raunin da aka yi injuries, Dogo Gide, sai da aka san yadda aka yi aka saci jiki aka shigar da shi asibiti a yankin Mabera a…
Read More
Yanzu-Yanzu: Kotu ta yanke wa ɗan China hukuncin kisa kan kisan Ummita a Kano

Yanzu-Yanzu: Kotu ta yanke wa ɗan China hukuncin kisa kan kisan Ummita a Kano

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Babbar Kotun Jihar Kano, ta yanke wa ɗan Chinan nan, Frank Geng Quarong hukuncin kisa ta hanyar rataya. Mai Shari’a Sunusi Ado Ma’aji ne ya yanke masa hukuncin, bayan tabbatar da hujjojin da masu gabatar da ƙara suka yi a gaban kotun. Idan za a iya tunawa Manhaja ta rawaito tun a ranar 16 ga watan Satumba 2022, Frank Geng, ya hallaka Ummita a unguwar Janbulo da ke jihar Kano.
Read More
Ɗaliban Kuriga sun shaƙi iskar ‘yanci

Ɗaliban Kuriga sun shaƙi iskar ‘yanci

Daga BASHIR ISAH Bayanai daga Jihar Kaduna na nuni da cewa, ɗaliban firamaren da aka yi garkuwa da su kwanan baya a yankin Kuriga a jihar, sun shaƙi iskar 'yanci. Gwamnan Jihar, Sanata Uba Sani, shi ne ya ba da sanarwar hakan a shafinsa na Facebook ranar Asabar da tsakar dare Idan za a iya tunawa, MANHAJA ta rawaito a ranar 8 ga Maris wasu 'yan bindiga suka kai hari yankin Kuriga, cikin Ƙaramar Hukumar Chilun a jihar Kaduna, inda suka yi awon gaba da yara sama da 200. Sai dai Gwamnan bai yi wani cikakken bayani kan sako yaran…
Read More
Hedikwatar Tsaro na neman su Dogo Gide, Simon Ekpa, Bello Turji da sauransu ruwa a jallo

Hedikwatar Tsaro na neman su Dogo Gide, Simon Ekpa, Bello Turji da sauransu ruwa a jallo

Daga BASHIR ISAH A ƙalla 'yan bindiga, ɓarayin daji da tsageru 97 ne Babban Ofishin Tsaro da ke Abuja ya bayyana a matsayin waɗanda yake nema ruwa a jallo. Ofishin ya ce waɗanda yake neman suna da hannu wajen aikata manyan laifuka da tada zaune tsaye a sassan ƙasa. Har wa yau, waɗanda lamarin ya shafa ya haɗa da shugaban wani ɓangare na tsagerun IPOB, wato Simon Ekpa. Mai magana da yawun rundunar soji, Manjo-Janar Edward Buba, shi ne ya bayyana sunaye da hotun waɗanda rundunar ke farautarsu. MANHAJA ta rawaito a makon jiya cewa, Babban Ofishin tsaro na shirin…
Read More
An sace fasinjoji a hanyar Ƙanƙara dake Katsina 

An sace fasinjoji a hanyar Ƙanƙara dake Katsina 

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Wasu ’yan bindiga sun yi sace fasinjoji da dama a wani harin da suka kai a Ƙaramar Hukumar Ƙanƙara da ke Jihar Katsina. Lamarin ya faru ne a jiya Alhamis bayan da ’yan bindigar dajin suka tare wata mota ƙirar bas mai cin mutane 18 mai lamba 14B-300-KT cike maƙil da fasinjoji mallakar hukumar kula da sufuri ta Jihar Katsina (KSTA). Wani ganau ya shaida wa majiyarmu ta wayar tarho cewa, galibin fasinjojin da ke cikin motar sun fito ne daga Ƙaramar Hukumar Funtuwa a kan hanyarsu ta zuwa Katsina, Babban Birnin Jihar Katsina.…
Read More
‘Yan binga sun sace mutum 61 a wani sabon hari a Kaduna

‘Yan binga sun sace mutum 61 a wani sabon hari a Kaduna

Daga BASHIR ISAH Rahotanni daga jihar Kaduna sun ce aƙalla mutum 61 wasu da ake zargin 'yan fashin daji ne suka yi garkuwa da su a yankin Buda da ke cikin Ƙaramar Hukumar Kajuru a jihar. Duk da dai babu bayani a hukumance ka aukuwar harin, sai dai wani mazaunin yankin ya shaida wa majiyarmu ranar Talata cewar, maharan sun dira ƙauyen ne da misalin ƙarfe 11:45 na dare inda suka yi awon gaba da mutum 61. A cewar Dauda Kajuru wanda mazaunin yankin ne, 'yan bindigar shiga yankin da yawansu, kuma sun harba bindiga. Ta bakinsa, “abin da ya…
Read More
Yanzu-yanzu: Majalisar Dattawa ta dakatar da Ningi na wata uku kan zargin cushen kasafi

Yanzu-yanzu: Majalisar Dattawa ta dakatar da Ningi na wata uku kan zargin cushen kasafi

Majailisar Dattawa ƙarƙashin jagorancin Sanata Godswill Akpabio, ta dakatar da Sanata Abdul Ningi na tsawon wata uku daga majalisar. Manlisar ta ɗauki wannan mataki ne yayin zaman da ta yi ranar Talata, kuma ta dakatar da Ningi ne bayan da ya yi zargin an yi cushe na Naira tiriliyan 3.7 cikin Kasafin 2024. A wata hira da BBC Hausa ta yi da ɗan majalisar mai wakiltar Bauchi ta Tsakiya kwanan nan, aka ji shi ya ce haƙiƙanin kasadin 2024 da aka gabatar Tiriliyan 25 amma ba Tiriliyan 28 da ake amfani da shi a halin yanzu ba. Ya ce bayan…
Read More
Ku yi wa Allah ku tallafa wa talakawan ƙasa, roƙon Tinubu ga su Ɗangote

Ku yi wa Allah ku tallafa wa talakawan ƙasa, roƙon Tinubu ga su Ɗangote

Daga BASHIR ISAH Shugaban Ƙasar Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya roƙi hamshaƙan 'yan kasuwar ƙasar, wato Aliko Dangote, Abdulsamad Rabiu da sauran masu ƙumbar susa, da su dubi Allah sannan su taimaka wa marasa galihu musamman a wannan wata na Ramadan. Tinubu ya yi wannan kira ne ranar Lahadi a Kano a wajen ƙaddamar da shinkafar da Santa Abdullahi Yari ya tanada don tallafa wa jama'a don girmamawa ga Shugaba Tinubu. Tinubu ya bayyana hakan ne ta bakin wakilinsa kuma hadiminsa, Abdulaziz Abdulaziz, inda ya yaba da karamcin da sanatan ya nuna masa. Ya ce an ƙaddamar da tallafin ne…
Read More
Ku nemi watan Ramadan daga ranar Lahadi — Sarkin Musulmi

Ku nemi watan Ramadan daga ranar Lahadi — Sarkin Musulmi

Daga BASHIR ISAH Sarkin Musulmi kuma Shugaban Majalisar Ƙoli ta Harkokin Musulunci a Nijeriya (NSCIA), Sa’ad Abubakar, ya buƙaci al'ummar Musulmi da a nemi jinjirin watan Ramadan na shekarar 1445AH daga ranar Lahadi, 10 ga Maris, 2024. Umarnin hakan na ƙunshe ne a sanarwar da ke ɗauke da sa hannun Farfesa Sambo Janaidu wanda ya kasance Shugaban Kwamitin Shawara na Majalisar Masarautar Sakkwato wadda aka raba wa manema labarai a ranar Asabar. Sanarwar ta ce: “Ana sanar da Al'ummar Muslim kan cewa su fara neman jinjirin watan Ramadan daga ranar Lahadi, 10 ga Maris wanda ya yi daidai da 29…
Read More