02
Mar
Daga AISHA ASAS A balin da ake ciki, maganin rigakafin xutar korona na AstraZeneca ya iso Nijeriya. Wannan shi ne rigakafin korona na farko da Nijeriya ta samu wanda ake sa ran za a yi wa 'yan ƙasa bayan gwamnati ta kammala tsare-tsarenta gane da rigakafin. Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari da mataimakinsa Yemi Osinbajo, za su tsayar da ranar da kowannesu zai yi allurar rigakafin cutar korona a idon duniya ta hanyar amfani da rigakafin Oxford/AstraZeneca na rukunin farko guda milyan 4 da Nijeriya ta karɓa a wannan Talata. Darakta a Hukumar Bunƙasa Kula da Lafiya na Matakin Farko na…