Ba duk shugaba zai kasadar Zulum ba – Buhari

*Shugaba Buhari ya gode wa ’yan Nijeriya da suke mara masa baya har yanzu

Daga NASIR S. GWANGWAZO a Abuja

Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya bayyana cewa, ba kowanne mai mulki ne zai iya yin irin kasadar da Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ke yi ba a cikin yanayi na matsalar tsaron da ke addabar jiharsa.

Shugaba Buhari, wanda ya ke jawabi a lokacin da ya ziyarci Fadar Shehun Borno jiya a ziyarar aikin da ya kai jihar ta Borno, ya yaba wa Gwamna Zulum bisa yadda ya ke wucewa gaba ba dare ba rana kuma cikin rashin tsoro tare da nuna turjiya duk da barazanar da ya ke fuskanta a yaƙin da ake yi da Boko Haram.

“’Yan ƙalilan ne daga cikin masu mulki za su yarda su riƙa fuskantar irin hatsarin da Gwamna Zulum ya ke fuskanta a ’yan shekarun nan, don kare al’ummarsa da kuma yauƙaƙa zaman lafiya da bunƙasar cigaba a yankinsa, musamman kan yadda ya ke jefa rayuwarsa cikin hatsari, inda ya ke zuwa ya kai dare tare da waɗanda balahirar rashin tsaro ta tagayyara,” inji Shugaba Buhari.

Da ya juya kan namijin ƙoƙarin nuna juriya da talakawan jihar ke yi da ma a ƙasa bakiɗaya, Shugaban Ƙasar ya gode wa al’umma bisa ba shi goyon baya da suke ci gaba da yi, duk da irin halin da ƙungiyoyi masu tayar da ƙayar baya a ƙasar suka jefa su a ciki.

A yayin da ya ka jaddada alƙawarinsa na ceto talakan Jihar Borno daga cikin wannan hali da ya tsinci kansa a ciki, Buhari ya tuno da cewa, a jihar ya fara ƙwarewa kan aikin soja ta fuskar riƙe muƙamin shugabanci a ƙarƙashin Gwamnatin Marigayi Janar Murtala Ramat Mohammed a matsayin gwamnan tsohuwar Jihar Borno, kafin daga bisani tsohon Shugaban Ƙasa, Janar Olusegun Obasanjo, ya na]a shi muƙamin Ministan Man Fetur.

Daga nan sai ya ƙara da cewa, yana kan yin duk mai yiwuwa wajen ganin ya saka wa ’yan ƙasar bisa irin goyon bayan da suke ba shi, domin a cewarsa, tamkar rance ne, wand dole ne a biya.

“Ina so ne na ga na biya bashin da ’yan Nijeriya suka ba ni na nuna ƙauna da soyayya a gare ni. Na fara riƙe mukamin siyasa a Maiduguri. Don haka a koyaushe zan riƙa waiwayen nana,” inji shi.

A lokacin da Gwamna Zulum ya ke jawabi, ya gode wa Shugaba Buhari bisa ziyarar da ya kawo, musamman don duba haƙiƙanin halin tsaron da jihar ke ciki da kuma ƙaddamar da ayyukan ci gaba da yi a jihar cikin ’yan shekarun da suka gabata.

A nasa jawabin, Mai Martaba Shehun Borno, Alhaji Abubakar Ibn Garbai El-Kanemi, shi ma ya gode wa Buhari bisa yadda a koda yaushe ya ke amsa kira kan halin da jihar ke ciki, yana mai cewa, hakan ya taimaka gaya wajen farfaɗowa da maganta matsalolin tsaro da jihar ke ciki.