Ko Boko Haram ta yi sabon shugaba ne?

Daga BARISTA BULAMA BUKARTI

A jiya ne dai wani sabon bidiyo da ya ke cire dukkan shakku game da mutuwar Shekau ya bayyana.

Wannan gajeren bidiyon ya ɗauko hoton mayaƙan ƙungiyar Boko Haram na ɓangaren tsohon shugabanta Abubakar Shekau. Inda suke ƙara tabbatar da mutuwar tsohon shugaban nasu.

Kakakin nasu mai suna Bakura Shalaba, ya bayyana tare da mayaƙa fiye da goma suna rufa masa baya. Inda ya yi addu’ar neman rahmar Allah ga Marigayi Shekau. Tare da kira ga ‘yan’uwan sa masu riƙe da makamai da kada su bari abinda ya faru ya kashe musu gwiwa.

Haka zalika, ya yi Allah wadai da Abu Mus’ab Al-Barnawi saboda kwatanta shi da mahaifin sa da Annabi Nuhu da ɗansa kafiri. Inda shi kuma ya kwatanta shi Barnawin da Shekau a matsayin Annabi Musa da Fir’auna.

Amma abu ma fi jan hankali shi ne, yadda ya bayyana cikakken goyon bayan sa ga ƙungiyar jihadi ta ISIS wadda takwararta ta ISWAP ta ce su ISIS ne suke ba wa Shekau umarnin kashe-kashen mutane.

Wannan bidiyon wata manuniya ce da take nuna har yanzu akwai ‘yar tsama ta ɓangaranci a tsakanin mayaƙan ƙungiyar JAS da kuma  takwararta ta  ISWAP. Kuma bisa dukkan alamu  takun saƙar nasu ba zai daidaita cikin kwanaki kaɗan ba.

Shalaba ya ƙarƙare jawabin sa da ƙaryata rarotannin da suke iƙirarin cewa kaso saba’in na mayaƙan JAS sun miƙa wuya ga ISWAP.

A halin yanzu dai ba a samu sahihin zance a kan waye zai gaji Shekau ɗin ba. Amma ana zargin ba zai wuce Bakura Doro ba.

Barista Bukarti, wanda lauya ne mai zaman kansa a Maiduguri, ya yi wannan rubutun ne a shafin sa na Facebook. Sani Ahmad Giwa ne ya fassara.