Rasuwar Attahiru ta hana murnar kisan Shekau

*Har yanzu rundunar sojan Nijeriya na ci gaba da taka-tsantsan
*Shin ko Nijeriya za ta amfana da nasarar ISWA kan Boko Haram?
*Janar Yahaya: Wane ne wanda Buhari ya saka magajin Attahiru?

Daga NASIR S. GWANGWAZO, a Abuja

A ranar Alhamis, 27 ga Mayu, 2021, rahotanni suka fantsama a cikin Nijeriya da ƙasashen duniya cewa, ɗaya da daga cikin waɗanda Nijeriya da Amurka ke kallo a matsayin manyan maƙiyanta kuma jagoran ƙungiyar masu tayar da ƙayar baya da aka fi sani da Boko Haram, wato Abubakar Shekau, ya rasa ransa a wani artabu tsakanin mabiyansa da mambobin ɗaya ƙungiyar ita ma mai tayar da ƙayar baya a Nijeriya da wasu yankunan Afrika ta Yamma da wani sashe na Afrika ta Arewa, wato The Islamic State in West Africa (ISWA), a mashuhurin dajin nan na Sambisa da ke Jihar Borno a Arewa maso Gabashin Nijeriya tun farkon makon.

Duk da cewa, har kawo yanzu ba a tabbatar da kashe shi ɗin, la’alla ko dai don ba a gawarsa ba ko kuma domin an saba bayar da rahotannin kisan nasa a baya, amma sai a wayi gari ya sake bayyana, amma dai duk da haka za a yi tsammanin murna ta kama mafi yawan ’yan Nijeriya da ma manyan ƙasashen duniya, idan aka zo da rahoton kashe shi ]in.

To, sai dai ƙasa da awanni 24 da bayyanar wancan labari, sai wani mummunan al’amari ya zo ya yi masa inuwa, wato mutuwar bakatatan da Babban Hafsan Sojojin Ƙasa na Nijeriya, Laftanar Janar Ibrahim Attahiru, a wani hatsarin jirgin sama a Kaduna ranar Juma’a, 21 ga Mayu, 2021.

Tabbas rasuwar ta girgiza ƙasar kuma ta mamaye batun lamarin mutuwar Shekau. Haka nan abubuwan da suka biyo bayan rasuwar Marigayi Janar Attahiru sun ƙara taimakawa wajen danne kururuwar kisan na Shekau ɗin koda ya zamo gaskiya. Misali a nan shine, rashin halartar Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari jana’izar Attahiru tare da mutane 10 ]in da suka rasu tare a cikin jirgin washegari, Asabar, a harabar Babban Masallacin Juma’a na Ƙasa da ke Abuja.

Nan da nan sai cece-kuce ya ɓarke kan batun, inda ake ta faman suka. Lamarin ya sake ɓaci ne a yayin da ɗaya daga cikin masu magana da yawun Shugaban Ƙasa ta ce, Shugaba Buhari bai iya halarta ba ne saboda a ƙa’idar tsaro ba ya fita daga Fadar Shugaban Ƙasa har sai ya samu rahoton tsaro awanni 48 kafin fitarsa, amma sai kuma Babban Mai Magana da Yawun Shugaban, Malam Garba Shehu, ya bayar da sanarwar da ta saɓa da hakan, yana mai cewa, Buhari ya ƙi zuwa ne, don kada ya haifar da cunkoson ababen hawa akan hanya, domin gudun kada ya jaza wa talakawansa ƙarin wahala. Wannan cin karo a bayanai, ya kawo ƙarin kace-nace a faɗin ƙasar.

Jim kaɗan bayan hakan kuma sai jita-jitar naɗa sabon Babban Hafsan Sojojin na Ƙasa ta kunno kai cikin awanni 48 da rasuwar wanda yake kai ]in. Har an fara haya-gaga da yi wa Fadar Shugaban Ƙasa cari kan hakan, saboda yadda aka san fadar da jan ƙafa a irin waɗannan abubuwa. To, amma sai katsam ta shammaci jama’a a jiya, Alhamis, 27 ga Mayu, 2021, ta sanar da Janar Yahaya Faruk a matsayin sabon babban hafsan. Nan da nan sai kallo ya koma sama.

Ire-iren faruwar hakan sun sanya ɗaukewar hankali daga batun zargin kisan Shekau da kuma bin ba’asin hakan. Bugu da ƙari, kasa fitowa da hedikwatar tsaro ta bayar da haske kan tabbacin kisan ko akasin hakan, ya sake rage kaifin batun, illa dai kawai cewa, da rundunar ta yi tana bincike, inda hakan ke nuna taka-tsantsan ɗinta kan lamarin.

Sai dai duk da wannan janye hankali da rasuwar Marigayi Attahiru da sauran dalilai suka haifar, manazarta na ta duban yanayin halin da ake ciki da kuma tasirin da kisan Shekau da ƙarfin da ISWA ta yi za su shafi yankin.

Ita dai ISWA ta ~alle ne daga Boko Haram a 2016 a }ar}ashin jagorancin Abu Musab al-Barnawi a ’yan shekarun baya, inda bayan kashe Shekau kuma ana zargin ta kama manyan kwamandojinsa kimanin 30, wan]anda ta ba su umarnin mi}a wuya da yin mubayi’a gare ta ko kuma ta kashe su kawai.

Ana ganin cewa, bayan ɓallewar ƙungiyar, ta ninka Boko Haram a mabiya da ƙarfi, inda ta ke da mayaƙa aƙalla tsakanin 3,500 zuwa 5,000, yayin da Boko Haram ke da tsakanin 1,500 zuwa 2,000.

Tabbas za a jira kuma a sanya idanu a ga ko ISWA za ta fi Boko Haram tasiri ko akasin hakan, to amma hakan ba zai hana a yi hasashen abubuwan da ka iya faruwa ba. Misali a nan shine, mamaye Boko Haram da ISWA ta yi na nufin masu tayar da ƙayar bayan za su tattara guri guda kenan, kuma za su riƙa karɓar umarni daga wuri guda, inda hakan ke nufin ha]in kai da zamowa tsintsiya maɗaurinki ɗaya.

A fili ta ke cewa, duk abin da ya dunƙule guri guda, ya fi ƙarfi da wahalar fasawa. Shin abin da zai faru kenan da ƙungiyar ISWA ko kuwa ragowar mabiya Shekau za su iya yi musu ƙafar ungulu? Lokaci ne ka[ai zai iya tabbatar da hakan.