Me ya kawo rabuwar auren Sani Danja da Mansurah Isah?

Daga MUKHTAR YAKUBU, a Kano

A ‘yan kwanakin nan babu abin da ya fi ɗaukar hankalin mutane kamar labarin rabuwar auren Sani Danja da Matarsa Mansurah Isah.

Labarin dai ya fara ne tun daga ranar Larabar da ta gabata, in da ita Mansurah ta bada sanarwa a shafinta na Instagram cewa ba su tare da mijinta Sani Danja. To sai dai ba ta yi wani ƙarin bayani ba, sannan kuma bayan ɗan wani lokaci da saka labarin sai ta yi sauri da goge shi. Bayan wannan kuma ba ta ƙara cewa komai ba a kan lamarin.

Wakilinmu ya yi ƙoƙarin samun ta a waya domin jin cikakken labarin, sai dai Mansurah Isah ba ta ɗaga kiransa ba. Sannan shi kuma Sani Danja da muka nemi jin ta bakinsa, shi ma ba mu samu cikakken bayani daga wajensa ba, domin cewa ya yi “tun da ita ce ta saka sai a je a nemi ƙarin bayani daga wajen ta.”

Maganar rabuwar Sani Danja da Mansurah Isah abu ne da ya zo wa mutane da ba zata, domin kuwa su ne a ke kafa hujja da su a cikin ‘yan fim a matsayin ma’aurantan da suka daɗe ba su rabu ba, kuma Allah ya yi musu arzikin yara har guda huɗu, mace ɗaya maza uku.

Sannan kuma a dai-dai lokacin da sakin ya faru suna kusa da cika shekaru 14 da auren na su, domin kuwa an ɗaura auren nasu ne a watan Yuni na shekarar 2006, sai kuma wannan ƙaddara ta faɗa musu.

Waata majiya da ke gidan Sani Danja ta tabbatar wa Manhaja cewar sakin ya faru ne a bayan ƙaramar Sallar nan da ta gabats, kuma tuni Mansurah Isah ta bar gidan da zama. Duk ƙoƙarin da muka yi don sanin abin da ya kai ga rabuwar ma’auratan, babu wani cikakken bayani.

Daman dai ba wannan ba ne karo na farko da suka fara rabuwa, domin kusan shekaru bakwai da suka wuce a baya Sani Danja ya taɓa sakin Mansurah Isah wanda suka ɗauki lokaci ba su tare da juna sai daga baya aka shirya, to sai dai a wancan lokacin da ya ke ba a yaɗa labarin ba, shi ya sa ba a sani ba.

Amma yanzu da ya ke maganar daga Mansurah Isah ta fito shi ya sa maganar ta yi saurin yaɗuwa kamar wutar daji, kuma hakan ya sa jama’a ba su ɗauki batun sakin da wasa ba.

Abin da mutane dai su ke ta yin fata shi ne Allah ya sa Sani da Mansurah Isah su koma su ci gaba gaba da rayuwa tare. Sai dai abin tunani a nan shi ne, babu tabbas a kan maganar komen ganin an taɓa yin sakin a baya, don haka yana da wahala a ce sakin bai Kai uku ba. Saboda in har ya kai uku to babu damar kome sai ta yi wani auren.

Wasu na ganin kamar sakin ukun ne shi ya sa Mansurah Isah ta sanar da cewar yanzu ba sa zaman aure da Sani Danja.
To ko ma dai mene ne yanayi da lokaci za su tabbatar da ko saki nawa aka yi, kuma da gaske sakin ya tabbata kamar yadda ita Mansurah Isah ta bayyana? Ko kuma dai hawa dokin zuciya ne irin na mata.

In dai sakin ya tabbata, to Sani Danja da Yakubu Muhammad, sun zama wasu manyan gwauraye a cikin masana’antar fina-finai ta Kannywood, domin Yakubu Muhammad ya shafe sama da shekaru biyar ba shi da mata yana zaman gwauranci, kwatsam sai ga Sani Danja shi ma ya bi sahunsa.