28
Jan
Daga FATUHU MUSTAPHA Hamshakin dan kasuwar nan na Kasar Amurka, Bill Gates, ya shawarci Nijeriya da ta karkatar da hankalinta zuwa ga inganta fannin lafiyarta maimakon kashe makudan kudade wajen sayo allurar rigakafin cutar korona. Gates ya ba da shawar ne a lokacin da yake ganawa da manema labarai ta bidiyo a Talatar da ta gabata, inda ya yi kira ga Nijeriya da kada ta yi amfani da 'yan kudaden da ta ware don kula da fannin lafiyarta wajen sayen rigakafin COVID-19 mai tsadar gaske. Jaridar Manhaja ta kalato dan kasuwar na cewa, “Ina mai bada shawarar a bai wa…
