02
Feb
Daga UMAR M. GOMBE Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya bayyana alhininsa dangane da rasuwar amininsa Prince Tony Momoh. A wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Femi Adesina ya fitar a Litinin da ta gabata a Abuja, Shugaba Buhari ya bayyana cewa, marigayin ya kasance tare da shi a duk faɗi-tashin da ya sha. Yana mai cewa, "Samun kwatankwacin marigayin wajen biyayya a fagen siyasa, abu ne mai wahalar gaske. Zan yi rashin sa matuƙa." Jaridar Manhaja ta kalato Buhari ya yi tuna baya inda ya ce, "Marigayi Momoh ya ba da gagarumar gudunmawa a matsayinsa na Shugaban Sashen Yaɗa…
