Babban Labari

Shugaban jaridun Manhaja da Blueprint ya sabunta rajistarsa a APC

Shugaban jaridun Manhaja da Blueprint ya sabunta rajistarsa a APC

Daga FATUHU MUSTAPHA A Juma'ar da ta gabata Shugaban Jaridun Manhaja da Blueprint, Alhaji Mohammed Idris Malagi, ya sabunta rajistarsa ta zama ɗan jam'iyyar APC a rumfar zaɓensa da ke Malagi, a ƙaramar hukumar Gbako da ke jihar Neja. Bayan kammala rajistarsa, Alhaji Idris ya yaba da yadda aikin yin rajistar ke guna cikin lumana a rumfar zaɓensu, tare da kira ga 'yan jam'iyyarsu ta APC a faɗin jihar kan kowa ya tabbatar da ya yi rajista ko sabunta rajistarsa. Yana mai cewa, "Na yi matuƙar farin ciki da yadda aikin yin rajistar ke gudana. Wannan wata alama ce mai…
Read More
Nijeriya za ta ƙirƙro rigakafin korona ba da daɗewa ba, cewar Minista Onu

Nijeriya za ta ƙirƙro rigakafin korona ba da daɗewa ba, cewar Minista Onu

Daga BASHIR ISAH Ministan Kimiyya da Fasaha Ogbonnaya Onu, ya ce nan ba da daɗewa ba Nijeriya za ta ƙirƙiro maganin rigakafin cutar korona don amfanin 'yan ƙasa. Ministan ya ce hakan zai samu ne ta dalilin tawagar ƙwararrun kimiyya da aka kafa ƙarkashin jagorancin Dr Oladipo kolawole na Jami'ar Adeleke, inda tawagar ke kan gudanar da bincikenta kan maganin cutar korona. Onu ya bayyana haka ne a Abuja a lokacin da ya karɓi baƙuncin wani kwamitin masana kimiyya a Abuja. Ministan ya yaba wa tawagar masu binciken daga Jami'ar Adeleke bisa sanya sunan Nijeriya a jerin ƙasashen duniya masu…
Read More
Galibin makiyayan da ke halaka mana mutane ba ‘yan Nijeriya ba ne, inji Ortom

Galibin makiyayan da ke halaka mana mutane ba ‘yan Nijeriya ba ne, inji Ortom

Daga BASHIR ISAH An bayyana cewa galibin makiyayan da ke halaka mutane a ƙasar nan ba 'yan asalin Nijeriya ba ne. Bayanin haka ya fito ne ta bakin Gwamna Samuel Ortom na jihar Binuwai yayin wani taron manema labarai da ya gudana a Abuja a ranar Alhamis da ta gabata. Ortom ya yi kira ga Shugaba Muhammadu Buhari da ya buƙaci a sake waiwayar dokokin ECOWAS don yin gyarar fuska dangane da sha'anin zirga-zirgar mutane da kayayyaki a nahiyar Afirka. Ya ce makiyaya daga wajen Nijeriya na amfani da damar zirga-zirga wajen ruruta matsalolin tsaro. Ta bakinsa, "Ƙasashe maƙwabta irin…
Read More
Buhari ya nuna alhininsa kan rasuwar Jakande

Buhari ya nuna alhininsa kan rasuwar Jakande

Daga FATUHU MUSTAPHA Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya nuna alhininsa dangane da mutuwar tsohon gwamnan jihar Legas, Chief Lateef Jakande, wanda Allah Ya yi wa cikawa a Alhamis da ta gabata. Sanarwar da ta fito ta hannun mai bai wa shugaban shawara kan sha'anin labarai da hulɗa da jama'a, Femi Adesina, Buhari ya ce marigayin ya yi rayuwa irin wadda al'umma ta amfana da ita. Sanarwar ta bayyana Jakande a matsayin mutum wanda ƙasa da al'umma suka amfana da rayuwarsa, wanda za a daɗe ana tunawa da kyawawan ayyukan da ya gudanar. Buhari ya miƙa ta'aziyyarsa ga iyalan marigayin gami…
Read More
Gwamnati ta amince da shirin kula da dattawa, inji Minista Sadiya

Gwamnati ta amince da shirin kula da dattawa, inji Minista Sadiya

Daga WAKILIN MU Majalisar Gudanarwa ta Tarayya (FEC) ta amince da sabon Shirin Kula Da Masu Manyan Shekaru ta Ƙasa, a turance 'National Policy on Aging', a matsayin wani ɓangare na ƙoƙarin da Gwamnatin Tarayya ke yi na tabbatar da tsaron lafiya da tattalin arzikin mutanen da yawan shekaru ya cim masu. Ministar Harkokin Jinƙai, Agaji da Inganta Rayuwa, Hajiya Sadiya Umar Farouk, ita ce ta bayyana haka ga manema labarai a Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja a ranar Laraba, jim kaɗan bayan taron hukumar, wanda Shugaba Muhammadu Buhari ya jagoranta. A cewar ta, manufar shirin ita ce domin…
Read More
Peters ya maye gurbin Farfesa Adamu a NOUN

Peters ya maye gurbin Farfesa Adamu a NOUN

Daga FATUHU MUSTAPHA Farfesa Olufemi A. Peters ya kama aiki a matsayin sabon Mataimakin Shugaban Buɗaɗɗiyar Jami'ar Nijeriya (NOUN) inda ya maye gurbin Farfesa Abdalla Uba Adamu wanda wa'adin aikinsa ya kammala a ranar Laraba, 10 ga Fabrairun 2021. Da yake jawabi yayin bikin karɓar ragamar aiki da ya gudana a ranar Alhamis a Abuja, Petaers ya bayyana cewa jami'ar ba za ta taɓa mancewa da gudunmawar da Adamu ya bayar wajen cigabanta ba a zamaninsa. Ya ce, "Zamanin Farfesa Adamu a jami'ar abu ne da ba za a manta da shi ba, kuma zai zama abin kwatance a gare…
Read More
Tsohon gwamnan Legas ya rasu

Tsohon gwamnan Legas ya rasu

Daga AISHA ASAS Allah ya yi wa gwamnan farar hula na farko a jihar Legas, Lateef Kayode Jakande rasuwa. Marigayin ya bar duniya yana da shekara 91. A halin rayuwarsa, Jakande wanda tohon ɗanjarida ne, ya yi gwamna a Jihar Legas daga 1979 zuwa 1983. Haka nan, ya riƙe muƙamin Ministan Ayyuka a zamanin mulkin marigayi Sani Abacha. An haifi marigayin ne a ranar 23 ga Yulin 1929, a Legas. Gwamnan Legas, Babajide Sanwo-Olu, ya nuna alhinin dangane da rasuwar, tare da bayyana marigayin a matsayin babban rashi.
Read More
‘Yan bindiga sun yi garkuwa da mutum 4 a Tungan Maje

‘Yan bindiga sun yi garkuwa da mutum 4 a Tungan Maje

Daga AISHA ASAS Wasu 'yan bindiga sun kai hari a Tungan Maje da ke yankin Gwagwalada, Abuja, inda suka yi garkuwa da wasu mutum huɗu. Al'amarin wanda ya auku a tsakar daren wannan Lahadin, sai da 'yan bindigar suka shafe kimanin sa'o'i uku suna abin da suka ga dama a Tungan Maje kafin daga bisani suka yi awon gaba da wani tsohon jami'in Hukumar Kula da Shige da Fice ta Nijeriya (NIS) Abdulahi Idris Rakieu da wasu mutum biyu daga iyalan gidansa. A cewar jaridar TheCable, harin ya shafi wani mai suna Olusola Agun, wanda shi ya zama cikon na…
Read More
Amnesty International na neman wargaza Nijeriya – inji Lai Mohammed

Amnesty International na neman wargaza Nijeriya – inji Lai Mohammed

Daga AISHA ASAS Gwamnatin Tarayya ta zargi Ƙungiyar Kare 'Yancin Ɗan-Adam ta Duniya (AI) da take-taken neman wargaza Nijeriya da gangar ta hanyar ɗora zarge-zarge a kan gwamnati da kuma sojoji. Ministan Labarai da Al'adu, Alhaji Lai Mohammed ne ya yi wannan zargi yayin wata hira da wata tashar talabijin ta yi da shi a Juma'ar da ta gabata a Legas wadda Hukumar Dillancin Labarai ta Nijeriya (NAN) ta bibiya. Ministan ya bayyana haka ne a matsayin martani ga wani rahoton ƙungiyar a kan yaƙi da batun take 'yancin ɗan-Adam a faɗin duniya inda ta nuna an yi zargin an…
Read More
Buhari ya zaɓi tsoffin hafsoshi a matsayin jakadu

Buhari ya zaɓi tsoffin hafsoshi a matsayin jakadu

Daga WAKILIN MU Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya miƙa sunayen tsoffin hafsoshin tsaron da suka yi murabus kwanan nan, ga Majalisar Dattawa domin amincewa da naɗa su a matsayin jakadu. A cikin wasiƙar da Buhari ya aika wa Sugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ahmad Ibrahim Lawan, Buhari ya ce, "Bisa la'akari da Kundin Tsarin Mulki sashe na 171 (1) da sashe na (2) (c) da ƙaramin sashe na (4) na Kundin Tsarin Mulki na 1999 na Tarayyar Nijeriya wanda aka yi wa gyaran fuska, ina mai gabatar da waɗannan sunaye guda 5 don neman amincewar Majalisar Dattawa kan yi musu naɗin…
Read More