22
Feb
Daga AISHA ASAS Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya bayyana alhininsa kan haɗarin jirgin saman sojoji da ya auku Lahadin da ta gabata a Abuja. Sanarwar da hadimin Buhari kan sha'anin yaɗa labarai, Femi Adesina ya fitar, ta nuna yadda Shugaba Buhari ya miƙa saƙon ta'aziyyarsa ga iyalai, 'yan'uwa da abokan aikin sojojin da suka rasu a haɗarin. Sanarwar ta ce Buhari ya bi sawun Rundunar Sojojin Sama ta Nijeriya da ma al'ummar Nijeriya baki ɗaya wajen makokin jami'an rundunar waɗanda ajalinsu ya cim musu a bakin aiki. Buhari ya ce an soma gudanar da bincike domin gano sababin haɗarin, tare…
