Babban Labari

An sako ɗaliban Sakandaren Kagara

An sako ɗaliban Sakandaren Kagara

Daga FATUHU MUSTAPHA Bayanai daga Jihar Neja sun nuna an sako ɗalibai da malamai na Sakandaren Kimiyya Kagara da 'yan bindiga suka yi garkuwa da su 'yan kwanakin da suka gabata. Wata majiya mai tushe ta tabbatar wa jaridar PRNigeria batun sakin ɗaliban a safiyar wannan Asabar. Idan dai za a iya tunawa, Manhaja ta ruwaito batun sace ɗaliban su 27 da ma'aikata 3 da iyalansu su 12, a ranar 17 ga Fabrairun 202.
Read More
‘Yan bindiga sun sace ɗalibai mata kimanin 300 a Zamfara

‘Yan bindiga sun sace ɗalibai mata kimanin 300 a Zamfara

Daga FATUHU MUSTAPHA Rahotanni daga Jihar Zamfara, sun nuna cewa 'yan bindiga sun sace ɗalibai mata kusan su 300 a Makarantar Sakandaren Gwamnati (GSS) Jangeɓe, da ke yankin ƙaramar hukumar Talata-Mafara a jihar, a tsakar daren Juma'a. Kwamishinan Labarai na jihar, Malam Suleiman Tunau Anka, ya tabbatar wa manema labarai faruwar haka, inda ya ce 'yan bindiga sun shiga makatar ne da misalin ƙarfe 1 na tsakar daren Juma'a suka kwashi ɗalibai. Sai dai Anka bai faɗi adadin ɗaliban da lamarin ya shafa ba. Wannan na faruwa a daidai lokacin da Gwamnan jihar Zamfara Bello Matawalle, ya yi kira ga…
Read More
Abuja: An yi jana’izar mayaƙan sama da suka rasu a haɗarin jirgin sama

Abuja: An yi jana’izar mayaƙan sama da suka rasu a haɗarin jirgin sama

Daga BASHIR ISAH An gudanar da jana'izar jami'an sojin saman nan su 7 da suka rasu a haɗarin jirgin sama da ya auku a Abuja a Lahadin da ta gabata. Jami'an da lamarin ya shafa sun cim ma ajalinsu ne bayan da jirginsu, ƙirar Beechcraft King Air 350, ya faɗo a ƙauyen Bassa daura da Babban Filin Jirgin Sama na Nnamdi Azikiwe, bayan da suka tashi da nufin zuwa aiki a jihar Neja. Mai Magana da Yawun Rundunar Sojin Sama na Nijeriya, Air Vice Marshal Ibikunle Daramola ya ce jirgin ya fuskanci matsalar inji kafin aukuwar haɗarin. Cikin waɗanda suka…
Read More
Majalisa ta tabbatar da naɗin sabbin jakadu duk da ƙorafin da aka yi a kan su

Majalisa ta tabbatar da naɗin sabbin jakadu duk da ƙorafin da aka yi a kan su

Daga WAKILIN MU Majalisar Dattawa ta tabbatar da naɗin tsoffin Shugabannin Tsaron Nijeriya a matsayin jakadu. Wanna ya faru ne a Talatar da ta gabata. Idan ba a manta ba, a Janairun da ya gabata Shugaba Buhari ya zaɓi General Abayomi G. Olonisakin da Lt. General Tukur Y. Buratai da Vice Admiral Ibok-Ete E. Ibas da kuma Air Marshal Sadique B. Abubakar don zama jakadun Nijeriya bayan murabus da suka yi daga aiki ba da jimawa ba. Amincewa da naɗin ya zo ne bayan gamsuwa da majalisar ta yi da rahoton kwamitin majalisar kan harkokin ƙasashen waje ƙarƙashin jagorancin Adamu…
Read More
EFCC ta yi sabon shugaba

EFCC ta yi sabon shugaba

Daga AISHA ASAS Majalisar Dattawan Nijeriya ta tabbatar da Abdulrasheed Bawa a matsayin sabon Shugaban Hukumar Yaƙi da yi wa Tattalin Arziki Zagon Ƙasa da Zambar Kuɗaɗe (EFCC). Sanatocin sun shafe sa'o'i biyu suna tantance Bawa kafin daga bisani suka tabbatar da shi a sabon matsayin nasa. Yayin da ake tantance shi, Bawa ya bai wa majalisar tabbacin cewa zai yi aiki tukuru don gyara wa hukumar zama ta hanyar inganta harkokinta kafin ƙarewar wa'adin jagorancinsa. Bawa ya ce zai yi aiki tare da waɗanda suka dace a sassan duniya domin tabbatar da Nijeriya ta amfana da dukiyoyinta da aka…
Read More
Ortom ya nemi Bala ya bai wa ‘yan ƙasa haƙuri kan furucinsa

Ortom ya nemi Bala ya bai wa ‘yan ƙasa haƙuri kan furucinsa

Daga AISHA ASAS Gwamnan Jihar Binuwai, Samuel Ortom, ya buƙaci takwararnsa na jihar Bauchi, Bala Mohammed, da ya fito ya bai wa 'yan Nijeriya haƙuri game da furucin da ya yi na goyon bayan Fulani makiyaya su riƙa amfani da bindiga wajen kare kansu. Ortom ya buƙaci haka ne yayin taron manema labarai da ya gudana a Makurdi a Litinin da ta gabata inda ya ce akwai buƙatar Gwamna Bala ya bada haƙuri domin sanyaya zukatan waɗanda suka rasa 'yan'uwa sakamakon ayyukan ɓatagarin Fulani makiyaya. Kazalika, Ortom ya buƙaci Gwamna Bala da ya yi koyi da takwarorinsa na Kano da…
Read More