*Sun fara yin shigar burtu
*Yanzu haka wani attajiri na hannunsu – Hon. Salihi
*Ku ci gaba da ba mu muhimman bayanai – ’yan sanda
Daga JAMIL GULMA a Sakkwato
Masu garkuwa da mutane sun ɓullo da sabon salon ɗaukar mutane a waɗansu sassan Jihar Sakwkwato, inda yanzu suka ɓullo da sabon salon ɗaukar mutane ɗaya-bayan-ɗaya a gidajensu, maimakon kai farmaki a cikin babbar tawaga.
Wakilin Manhaja mai kula jihohin Sakwkwato da Kebbi ya ziyarci waɗansu yankuna da suka haɗa da ƙananan hukumomin Illela, Gada da kuma Gwadabawa, inda abin ya fi ƙamari.
Shugaban Ƙaramar Hukumar Illela, Hon. Injiniya Aliyu Salihu, ya bayyana cewa, gaskiya ne yanzu waɗannan mutane sun ɗauki sabgar kai samame a gidajen mutane, inda kai tsaye sukan yi awon gaba da mutum cikin ruwan sanyi ba tare da wata hayaniya ko harbe-harbe ba.
Ya ƙara da cewa, “yanzu haka akwai wani ɗan kasuwa mai suna Alhaji Jadi Gaidau da suka je gidansa a daren Talatar da ta gabata a ƙauyen Gaidau da ke Ƙaramar Hukumar Illela suka ɗauke shi, suka tafi da shi, kuma har zuwa yau ba wani labari, saboda ba wanda suka kira, don neman kuɗin fansa ko kuma wani bayani.”
Hon. Salihu ya ce, “sauya salon ɗaukar mutane, don neman kuɗin fansa ko garkuwa da waɗannan ɓatagari suka yi, ba zai rasa nasaba da irin ƙwarin gwiwar da hukumomi ke bai wa al’ummomi na tunkarar mahara ba a duk lokacin da suka kai hari a garuruwansu, wanda a gaskiya ya yi tasiri saboda kafin su ɓullo da wannan sabuwar hanyar, an ɗauki lokaci mai tsawo ba a sami labarin kai farmaki wannan yankin ba.”
Ya kuma ƙara da cewa, hukumomi ba za su yi ƙasa a gwiwa wajen nemo bakin zaren daƙile wannan hanyar ba ita ma. Don haka ya yi kira ga al’ummomi da kada su ma su yi ƙasa a gwiwa wajen sanar da hukumar da ta fi kusa da su duk wani mutum ko waɗansu gungun mutane da ba su yarda da su ba.
Wakilinmu ya yi tattaki har ƙauyen na Gaidau, inda ya nemi jin ta bakin iyalan ɗan kasuwar da suka kama, amma dai hakan ba ta samu ba, saboda yanayi na damuwa, amma dai wani daga cikin ’yan uwansa, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya bayyana cewa, ranar Litinin dai mutanen garin suka wayi gari da samun wannan labarin na wa]ansu ’yan bindiga sun zo sun tafi da shi (Alhaji Jadi), amma sai dai ba wata hayaniya ko harbe-harbe. Yanzu haka dai suna nan suna jira ko da mutanen za su bugo waya.
Bayanai da Wakilin Manhaja ya tattara daga wannan yankin na ƙananan hukumomin Illela, Gada da kuma Gwadabawa sun nuna cewa, yanzu haka kusan duk safiya ta Lillahi sai an shiga wani ƙauye an ɗauki mutane, amma sai dai cikin ruwan sanyi a ke wannan ta’asar.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ’yan sanda ta jihar Sakwkwato, Mataimakin Sufurtandan ’Yan Sanda, Abubakar Sanusi, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya bayyana wa Wakilinmu cewa, “ranar 9 ga wannan watan da daddare an yi artabu tsakanin ’yan sanda da ke sintiri a wannan yankin a ƙarƙashin jagorancin Mataimakin Kwamishinan ’Yan Sanda, Aliyu Akilu Raba, inda maharan suka gudu da raukuka sai dai sun lalata motar ’yan sanda a cikin musayar wutar, sannan kuma ba wanda ya ji rauni daga ɓangaren ’yan sanda.”
Ya ƙara da cewa, akwai rahoton sace matan wani Alhaji Hassan Takalmawa, inda bayyana cewa, yanzu haka rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Sakwkwato tana nan tana aiki ba dare ba rana wajen bin diddigin kamo waɗannan ɓatagari.
Ya kuma yi kira ga al’umma da su riƙa kai rahoton duk wani abu ko mutane da su ke da shakku game da su, saboda aikin tsaro ba na hukumar ’yan sanda ba ne kaɗai, amma dai su daina ɗaukar doka a hannunsu.