Rikicin Tiwita: An bar jaki, ana dukan taiki

A makon jiya ne, Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya aike da wani
kakkausan saƙo ga waɗanda suka addabi ƙasarsa da fitinar tsaro ta hanyar kashe rayuka, ɓarnata dukiya da kai wa ofisoshin gwamnati hare-hare. Shugaban yana mayar da martani ni kai-tsaye kan ƙungiyar ’yan ta’addar nan ta IPOB mai fafutukar kafa Ƙasar Biyafra, wacce a kwanakin nan ta ke kai hare-haren ta’addanci kan ofisoshin hukumar INEC da na ’yan sanda a yankin Kudu maso Gabas. Shugaba Buhari ya kuma yi furucin ne a Fadar Shugaban Ƙasa lokacin da Shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu, ya kai masa ziyara, inda ya kai kuka ga Shugaban Ƙasar kan halin barazanar tsaro da hukumar ke fuskanta.

A cikin jawabin nasa, kakkausan furucin da Buhari ya yi a lokacin ziyarar, inda ya ke cewa, “da yawan waɗanda a yau suke aikata wannan aika-aika ba su da girman shekarun da za su san irin lalatawa da asarar rayukan da suka faru a lokacin Yaƙin Basasar Nijeriya ba.

Daga cikinmu, waɗanda suka kasance a fagen daga tsawon watanni 30, za su ɗauki mataki akansu ta hanyar irin yaren da suka fi fahimta,” shine furucin da ya janyo cece-kucen kuma shine, kalamin da ya janyo Tiwita ta cire saƙon daga manhajarta. To, amma muhimmin abin da Shugaba Buhari ya tattauna a kai shine, batun tsaron ƙasa, wanda ya haɗa da rayuka da dukiyoyin al’umma da kuma kadarorin gwamnati, wanda su ma mallakar ’yan ƙasa ne.

A cikin jawaban nasa ya ce, “yau na amshi bayani daga Shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta (INEC) kan jerin hare-haren da ake kai wa kadarorinta a faɗin ƙasar. Waɗannan hare-hare ba abubuwan amincewa ba ne, kuma ba za mu bar masu ɗaukar nauyinsu ba su cimma mummunar aniyarsu. Na bai wa Hukumar INEC tabbacin cewa, za mu ba su dukkan abin da suke buƙata, don su gudanar da aikinsu yadda ya kamata, don kada ma wani ya ce, ba mu son barin mulki ko kuma mu na son zarcewa zango na uku. Babu wani uzuri abin karba ga kasawa. Za mu biya wa INEC dukkan buƙatunta.

A ɓangaren tsaro, mun canja Shugabannin Tsaro da Babban Sufeton ’Yan Sanda na Ƙasa, kuma mun umarce su da su tabbatar sun tashi-tsaye wajen ganin sun fuskanci ƙalubalen da ke gabanmu. Ba sauran uzuri kan waɗanda suke faman ganin sun ɗaiɗaita ƙasarmu ta hanyar haɓaka ayyukan laifi da ta’addanci.”

Daga nan ne sai Shugaba Buhari ya rufe kalamansa da waccan barazana, wacce ba kasafai ya ke yin irinta ba, inda ya yi hannunka mai sanda da cewa, masu aikata ta’addanci a kadarorin hukumomi da ofisohsinsu su ma za su fuskanci irin abin da suke aikatawa daga ɓangaren gwamnati.

Babban abin takaici a cikin wannan lamari shine, yadda cire saƙon Shugaba Buhari a manhajar ta Tiwita ya ɗauke hankalin komai. A ɓangaren gwamnati ta tattara ƙarfinta ne ga mayar da martani kan cire saƙon Shugaban Ƙasar.

Da yawan masu nazari ba su yarda da matakin Tiwita na cire saƙon Buhari ba, domin yana mayar da martani ne kan wani ta’addanci da a ke aikata wa bil adama a ƙasarsa kuma kowa ya sani cewa, babu wani shugaba nagari da zai zura idanu yana gani a na halaka rayuka ko dukiyoyin al’ummarsa ba tare da ya ]auki matakin komai ba. Don haka matakin da Tiwita ta ɗauka kan sa}on nasa ya janyo mata suka mai zafi.

To, amma sanarwar da Ministan Yaɗa Labarai na Nijeriya, Lai Mohammed, ya bayar na dakatar fa manhajar ta Tiwita a Nijeriya, ya rage karsashin gwamnati a idanun manazarta kuma ya taimaka gaya wajen ɗauke hankalin ita kanta gwamnati ga ɗaukar matakan da shi Shugaba Buhari ya ci alwashin ƙauka kan masu aikata wancan ta’addanci.

Kawo yanzu ba a samun bayanan komai illa sanarwa daga gwamnati a ƙoƙarinta na tabbatar da cewa, ta cika wancan buri na dakatar da Tiwita, alhali abin da ya fi dacewa ta mayar da hankali a kai shine, kawo ƙarshen ayyukan ’yan IPOB da suke addabar ƙasa da al’ummarta.

Su kansu al’umma da sauran manazarta da ke matsa wa gwamnati lamba kan tabbatar da cewa, ta kawo ƙarshen ire-iren waɗancan ayyukan ta’addanci da IPOB da makamantanta ke yi, sun yi sako-sako wajen cigaba da hakan, inda suka koma nazarce-nazarce da yin sharhi kan batun Badaƙalar Tiwita.

Abin da ya fi dacewa a mayar da hankali a kai shine, batun shawo kan matsalolin tsaron da suka addabi ’yan ƙasa, waɗanda su ne ummal’aba’isan wancan kyakkyawan furuci na Shugaba Buhari, wanda Tiwita ta cire. Damuwa kan batun cire saƙo a Tiwita ba shine abin da ya damu ’yan ƙasa ba, duk da cewa, wasu na kallon batun a matsayin raini ga shugaban ’yantacciyar ƙasa, wanda hakan ke nuna ƙasƙanta ita kanta ƙasar.

To, amma ga wanda ya san gaskiyar yadda Tiwita ke tafiyar da ayyukan ƙa’idojinta zai iya gane cewa, ba ta da wani tartibin abu da don ta cire saƙonka, hakan zai zama ƙarƙanci a gare ka, domin abin da ta ke dogara da shi wajen cire saƙo bai wuce kai mata rahoton koke akan saƙon mutum ba.

Abin nufi a nan shine, komai kyan saƙonka a manhajar Tiwita, idan mutane da yawa suka taru suka yi ta tura mata da rahoton ƙorafi akan saƙon, to za ta iya cire shi. Don haka za a iya cewa, abin da ya faru shine, bayan da Shugaba Buhari ya aike da saƙon, sai wasu masu adawa da ƙunshin saƙon suka duƙufa wajen aike wa da wancan ƙorafi.

Ita kuma Tiwita ba ta da tsari na idan an aika da saƙon ƙorafi, to akwai kuma dama ta aika wa da saƙon goyon baya. Ba ta da wannan tsari, domin ita ƙorafi kawai ta sani. A taƙaice ma dai ba ta aiki da yawan waɗanda suka nuna son su ga saƙon (wato ‘likes’) wajen yanke wancan hukunci na cire saƙo a Tiwita.

To, bisa la’akari da wannan, za a iya cewa, ya kamata Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta gane cewa, ba naƙasu ba ne ga Shugaba Buhari, don an cire saƙonsa a Tiwita, domin shi ba Shugaba Trump ba ne da za a iya cewa, mafi yawan jama’a ba su tare da saƙon da ya aike kuma ba labaran ƙarya ya aike da su ba, saɓanin zargin da aka yi wa Trump.

Don haka mayar da hankali kan cika alƙawarin da Buhari ya yi shine abin da ya fi dacewa, maimakon a zauna har sakaci ya sanya waɗancan ’yan ta’adda na IPOB su ci gaba da fafutukarsu ta hanyar gallaza wa jama’a, ɗaukar rayukansu da ɓarnata dukiyoyinsu!