Wasu malamai da ɗaliban Nuhu Bamalli Polytechnic sun faɗa hannun miyagu a Kaduna

Daga UMAR M. GOMBE

‘Yan bindiga sun yi garkuwa da wasu malamai da ɗaliban makarantar Nuhu Bamalli da ke Zariya a jihar Kaduna.

Bayanan da Manhaja ta kalato sun nuna lamarin ya faru ne da daddare a Alhamis da gabata, inda aka yi garkuwa da mutane a ƙalla su takwas.

Binciken Manhaja ya gano cewa daga cikin waɗanda aka sace akwai malamai da ɗalibai da iyalin wani malamin makarantar.

Bayanai sun ce wani ɗalibi guda ya rasa ransa yayin harin sakamakon harbin bindiga yayin da wani ya samu rauni.

Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kaduna, Samuel Aruwan, ya tabbatar da faruwar lamarin, tare da cewa jami’an tsaro ba su yi nawa ba wajen bayyana a makarantar bayan da labari ya isa gare su.

Sai dai Kwamishinan bai bayyana adadin mutanen da lamarin ya rutsa da su ba.

Babu wata tazara sosai a tsakanin Nuhu Bamalli Polytechnic da sansanin sojoji da ke Jaji a Kaduna.

Kwanan nan ne dai aka ji matar gwamnan jihar Kaduna, Hajiya Asia El-Rufai, ta fito ta yi kira ga ‘yan Nijeriya da su zamo masu sadaukar da ransu domin kawo ƙarshen matsalar garkuwa da mutane a faɗin ƙasa.

Tana mai cewa, “A shirye nake in rasa raina a hannun masu garkuwa da mutane muddin hakan zai haifar da zaman lafiya.”