Arahar fetur ta yi yawa a Nijeriya – NNPC

*Ya kamata farashin fetur ya kai Naira 256 duk lita
*Nijeriya na kashe Naira biliyan 150 duk wata kan tallafin mai – Mele Kyari
*Nijeriya ba za ta iya jure biyan tallafin mai ba, inji shi

Daga NASIR S. GWANGWAZO a Abuja

Babban Manajan Darakta na kamfanin kula da mai na Nijeriya (NNPC), Malam Mele Kyari, ya bayyana cewa, bisa la’akari da irin kuɗin da Nijeriya ke kashewa wajen shigo da tataccen man fetur a ƙasar, za a iya cewa, farashinsa na Naira 162 a gwamnatance ya yi matuƙar kaɗan, yana mai cewa, aƙalla ya kamata a sayar da shi kan Naira 256, idan ana so Nijeriya da ’yan ƙasar su daina asarar da su ke sha kan tallafi man na fetur.

Kyari ya bayyana hakan ne a wani taron da kamfanin NNPC ya shirya a Abuja, don maganin matsalar fasa}waurin fetur.

A yayin da ya ke magana kan biyan kuɗin tallafin mai, Kyari ya nusar da cewa, an yi ƙididdigar lissafin farashin man fetur kan yadda ya dace a sayar da shi ne bisa la’akari da yadda farashin kuɗi ya ke a kasuwar shunku ta duniya.

“Idan da za mu sayar da fetur bisa la’akari da farashin kasuwar shunku a halin yanzu, za mu sayar da shi ne kan Naira 256 bisa kowacce lita. Abin da mu ke sayarwa a halin yanzu shine Naira 162. Ƙasar ce ta ke yin asarar ratar da aka samu,” inji shi.

Daga nan sai ya bayyana cewa, a haƙiƙanin gaskiya Nijeriya ba za ta iya jure ci gaba da biyan tallafin mai ba, saboda yawan da ya ke da shi, idan aka yi la’akari da yadda ya kai har Naira biliyan 150 duk wata.

Shugaban na NNPC ya ƙara da cewa, “matuƙar ba mu yi taka-tsantsan kan yawan abin har zuwa lokacin da za mu fita daga matakin da muke a yanzu ba, wanda na san cewa ana yin aii tuƙuru kan hakan, to sai dai mu yi taka-tsantsan kan adadin farashin na tsakanin Naira 16 2 zuwa 256. Bambancin yana kai-komo ne tsakanin Naira biliyan 140 zuwa 150 akan ƙasar duk wata.

“Matuƙar adadin yana ƙaruwa, to kuɗin ma ƙaruwa suke yi, kuma muna fama da ɗawainiya guda biyu da muke fuskanta; ɗawainiyar kawo man da ɗawainiyar canjin kuɗin ƙasar waje ga kamfanin NNPC. Ba lallai ne mu samu cakin canjin ku]i na ƙasar waje na yiwuwa wajen shigo da kayan ba.”