Yawaitar laifuka a Nijeriya ya wuce minsharrin – Ganduje

Daga AMINA YUSUF ALI

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano ya bayyana cewa, afkuwar laifuka a jihar Kano, shi ma ya haura ya zuwa mataki na gaba. Wato dai ya wuce hankali.

Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin da yake karɓar baƙuncin Sufeto Janar na hukumar ‘yansanda, Usman Baba a jihar Kano. Gwamnan ya ƙara da cewa, idan za a kula, za a ga ya baza na’urorin leƙen asiri CCTV a ko’ina a jihar Kano. Saboda kare rayuka da dukiyoyin al’ummar jihar.

Ganduje ya bayyana cewa tunda su ma afkuwar laifuka sun yawaita, dole ne a samo karen bana wanda zai magance zomon bana. Wato dole a samo wasu hanyoyi masu ƙarfin daƙile waɗnnan laifuka da suke ta ƙara yawaita.

Ganduje ya ci gaba da cewa, tuni kyamarorin leƙen asirin suka bazu ko’ina a jihar Kano abinda ya rage yanzu kawai yadda za a saita na’urar ta kama aiki yadda ya kamata.

Haka nan, ya ce a halin yanzu ma an samar da na’uarar bibiya (tracker) wacce za ta dinga aiki a ƙofar shiga birnin. Sannan kuma an gina sansanin jami’an tsaro daban-daban domin samar da tsaro a ƙofofin shiga garin Kano.

A yayin da Ganduje ya tarbe shi, Usman Baba ya bayyana wa Gwamnan cewa, ya shigo Kano ne domin wasu shirye-shirye da suke da nasaba da bikin yaye ɗaliban Makarantar Horas da ‘Yansanda ta Nijeriya da ke ƙaramar hukumar Wudil a Jahar.