Me ya sa DSS ta gayyaci Sheikh Gumi?

Bayanan da Manhaja ta samu sun nuna hukumar tsaro ta DSS ta gayyaci fitaccen malamin nan, wato Sheikh Ahmed Gumi.

Duk da dai ba a bayyana dalilin gayyatar da DSS ta yi wa malamin ba, amma dai ya tabbata cewa ta gayyace shi.

Sai daiwasu ‘yan ƙasa na ra’ayin cewa gayyatar ba ta rasa nasaba da yadda malamin ke ƙoƙarin ziyartar ‘yan fashin dajin da suka addabi sassan ƙasa tare da bai wa gwamnatin shawarwari don samun masla.

Mai magana da yawun DSS,, Dr. Peter Afunanya, ya tabbatar wa jaridar The Fender cewa gaskiya ne cewa hukumarsu ta gayyaci Sheikh Gumi.

Gayyatar wadda aka yi ta ranar Juma’a, Afunanya ya ce bai saɓa ƙa’ida ba DSS ta gayyaci duk mutumin da take da buƙatar jin ta bakinsa kan wani al’amari.