Ƙungiyar Matasan Arewa ta nemi tubarrakin Kansilan Kano

Daga SANI AHMAD GIWA

A jiya Juma’a 25 ga Yuni, 2021, ne wata ƙungiyar matasan Arewa mai suna Arewa Youths Elites Initiative ta yi tattaki tun daga Kaduna ta kai wa fitaccen kansilan nan na Kano mai mataimaka 18, Hon. Muslihu Yusuf Ali, ziyarar ban girma da neman tubarraki, inda ta miƙa ma sa takardar naɗa shi Uban Ƙungiya (wato Grand Patron), saboda shi himmarsa da ƙoƙarinsa wajen inganta rayuwar al’umma, musamman ma matasa.

Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa, wacce Kakakin yaƙin neman zaɓen kansilan, Muhseen Tasiu Yau, ya fitar a jiyan, ya na mai tabbatar da cewa, tuni dai Hon. Muslihu Ali ya amince da wannan muƙami kuma har ya rattaɓa hannu kan takardar amincewa da hakan a lokacin da ya amshi tawagar ƙungiyar a ofishinsa da ke Tudun Maliki a cikin Birnin Kano.

Sanarwar ta ci gaba da cewa, a yayin ganawarsa da su kuma, Kansilan Kano ya tattauna da tawagar kan muhimman batutuwa game da matasa da kuma hanyoyin da za a bi wajen shawo kan matsalolinsu, musamman a Arewa.

A tare da shi kansilan yayin ziyarar akwai masu taimaka masa, kamar P.A Sulaman, SSA Babawo, PPS Abba Abdu Yahaya, SSA Mal Usama Umar da sauran na hannun damansa.