Da ɗuminsa: Buhari ya soke tafiya duba lafiyarsa a Landon

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya dakatar da tafiyar da ya kamata ya yi yau Juma’a zuwa Birnin Landon domin duba lafiyarsa.

A bayanin da mataimaki na musamman ga Shugaban Ƙasar kan yaɗa labarai, Femi Adesina, ya fitar ya ce za a sanar da wata ranar da ta dace domin tafiyar.

Sai dai a bayaninsa bai sanar da dalilin dakatar da tafiyar ba, lamarin da ‘yan Nijeriya da dama ke son sani, kasancewar ruwa ba ya tsami banza.