Ganduje zai gina gidaje 5,000 ga malaman makaranta

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Gwamnan Jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya sanya hannu a kan yarjejeniyar fahimtar juna tsakanin gwamnatin Kano da wani kamfani mai zaman kansa, da nufin gina gidaje 5,000 ga malaman makaranta a jihar.

Rahotanni sun tabbatar da cewa an cimma wanan matsaya ne yayin wani taro da aka gudanar a masaukin gwamnonin ƙasar nan da ke rukunin gidaje na Asokoro a Birnin tarayya Abuja. Yayin wannan taron da kamfanin, Gwamna Ganduje ya na tare ne da Sanatocin Kano guda 3, kwamishinoni, ‘yan majalisu da sauran muƙarraban gwamnati.

Sakataren yaɗa labaran Gwamnan, Malam Abba Anwar, shi ne ya sanar da hakan cikin wata sanarwa da ya aike wa manema labarai a jiya Alhamis, ya na mai cewa wannan yunƙuri na daga cikin alƙawarin da gwamnan ya yi wa malaman na ganin ya samar musu da tsarin ba su muhalli.

Shi ma a nasa jawabin, shugaban Ƙungiyar Malamai ta Ƙasa (NUT) reshen jihar Kano, Muhammad Hambali, ya gode wa Gwamnan bisa wannan ƙoƙari nasa, tare da nuna jin daɗi kan yadda gwamnan ke ci gaba da bayar da muhimmanci ga walwalar malaman makarantun jihar Kano.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *