Dalilin da ya sa Buhari bai halarci jana’izar attahiru ba – Fadar Shugaban Ƙasa

Daga UMAR M. GOMBE

Shugaban Ƙasa Muhammad Buhari ya bayyana dalilin da ya sa bai samu halartar wurin jana’izar tsohon Shugaban Rundunar Sojoji, Lt. Gen. Ibrahim Attahiru tare da wasu jami’ai 10 da aka gudanar a ranar Asabar da ta gabata.

Attahiru da sauran jami’ai goma sun cim ma ajali ne a haɗarin jirgin saman da ya rutsa da su a Juma’ar da ta gabata a Kaduna.

A cewar Fadar Shugaban Ƙasa, Shugaba Buhari na buƙatar bayanan tsaro na aƙalla sa’o’i 48 kafin ya ba fadarsa don halartar kowane irin taro.

Da alama dai rashin ganin Buhari a wajen taron jana’izar hakan bai yi wa wasu ‘yan ƙasa daɗi ba, lamarin da ya sanya wasunsu suka zarge shi da rashin tausayi.

Hadimar Shugaban Ƙasar Kan Sha’anin Soshiyal Midiya, Lauretta Onochie, ta bayyana a shafinta na twita a Litinin cewa, “Kafin Shugaban Kasa ya halarci jana’iza ko wani taro a wajen Fadar Shugaban Ƙasa, wajibi ne a tattara bayanan tsaro game da wurin sa’o’i 48 kafin taron kamar yadda tsarin tsaro ya buƙata.

“Idan ya zamana Babban Hafsan Hafsoshi tare da tawagarsa sun rasu jiya kuma za a yi musu jana’iza yau, ba za a sa ran Shugaban Ƙasa ya halarci wurin taron da ba a tattaro bayan tsaro a kansa ba.”

Ta ci gaba da cewa, “Ba a cim ma mafi ƙarancin sa’o’in 48 da ake buƙata ba. Game da sha’anin tsaro kuwa, tarurrukan jana’iza wurare ne da manyan ‘yan siyasa kan fuskanci haɗari.

“Sannan batun tsaro da kuma bai wa Shugaban Ƙasa kariya abu ne da ba a yin sa da son zuciya. Akwai dokoki da ya zama wajibi a kiyaye su.”