HOTO: Ɗaliban FUAA sun yi zanga-zanga sakamakon sace wani ɗalibi da ‘yan bindiga suka yi

Sakamakon sace Olayinka Toyinbo, ɗan aji huɗu (400L) a Jami’ar Nazarin Harkokin Noma ta Tarayya da ke Abeokuta, jihar Ogun da ‘yan bindiga suka yi, hakan ya haifar da ɗaliban jami’ar gudanar da zanga-zangar lumana don nuna rashin jin daɗinsu kan abin da ya faru da ɗan’uwansu, tare kuma da neman a sako shi.