‘Yan bindiga sun sace matar shugaban matasan APC a Oyo

Daga WAKILINMU

Wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne, sun sace matar shugaban matasa (youth leader) na jam’iyyar APC a jihar Oyo a yammacin Lahadin da ta gabata.

Bayanan da Manhaja ta kalato sun nuna an sace matar Dr Adenike Oni-Salawu ne a gaban gidansu da ke yankin hanyar tsohuwar Ife a Ibadan.

A daidai lokacin da matar ta sauka a motarta sannan take ƙoƙarin buɗe get don ta shige gida sai ‘yan bindigar suka yi amfani da wannan dama suka far mata ɗauke da muggan makamai tare da yin awon gaba da ita.

Wata majiya ta kusa da shugaban matasan na APC, ta ce an kai rahoton aukuwar lamarin ga ofishin ‘yan sanda da ke Gbagi Sabuwa a yankin.

Sai dai, ya zuwa haɗa wannan labarin hukumar ‘yan sandan jihar ba ta kai ga cewa komai game da lamarin ba.