11
Jun
*Sun fara yin shigar burtu*Yanzu haka wani attajiri na hannunsu – Hon. Salihi*Ku ci gaba da ba mu muhimman bayanai – ’yan sanda Daga JAMIL GULMA a Sakkwato Masu garkuwa da mutane sun ɓullo da sabon salon ɗaukar mutane a waɗansu sassan Jihar Sakwkwato, inda yanzu suka ɓullo da sabon salon ɗaukar mutane ɗaya-bayan-ɗaya a gidajensu, maimakon kai farmaki a cikin babbar tawaga. Wakilin Manhaja mai kula jihohin Sakwkwato da Kebbi ya ziyarci waɗansu yankuna da suka haɗa da ƙananan hukumomin Illela, Gada da kuma Gwadabawa, inda abin ya fi ƙamari. Shugaban Ƙaramar Hukumar Illela, Hon. Injiniya Aliyu Salihu, ya…
